Tsohon Shugaban Ƙasar Misra, Mohammed Mursi ya faɗi yayinda ake sauraron ƙara a kotu, ya kuma mutu, kusan shekara shida bayan an tumɓuke shi daga shugabanci a wani juyin mulki da aka zubar da jini.
Morsi, ɗan shekara 67, yana halartar zaman kotu ne a ƙarar da ake sauraro ranar Litinin, yayinda ya yanke jiki ya faɗi, ya kuma mutu, a cewar kafar yaɗa labarai ta gwamnati.
“Ya tambayi alƙali cewa yana so ya yi magana, kuma an ba shi dama. Bayan an ɗaga sauraron ƙarar, sai ya faɗi ya suma, kuma ya mutu. Daga nan sai aka kai gawarsa asibiti”, in ji jaridar Gwamnatin Misra, Al-Ahram.
Morsi ya zama Shugaban Ƙasa ne a shekara ta 2012, biyo bayan zaɓen Misra na farko da ake ganin an yi adalci, bayan an kori Hosni Mubarak daga mulki. Ya yi nasara ne da kaso 51 cikin ɗari, kuma mulkinsa shi ya farfaɗo da Ƙungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta Misra, wadda ta yi aiki tsawon shekaru a matsayin jam’iyyar siyasa ta ƙarƙashin ƙasa.
Sai dai shekara ɗaya bayan nan aka kawo ƙarshen mulkinsa, bayan da aka ci gaba da zanga-zanga a kan tituna, wannan lokacin don a kawo ƙarshen mulkin Morsi. Bayan nan, Dakarun Sojin Misra sun ƙwace mulki a wani juyin mulki da suka yi ranar 3 ga watan Yuni, 2013, juyin mulkin da yasa Ministan Tsaro na lokacin, Abdel- Fatah al-Sisi ya zama Shugaban Ƙasa.
A matsayin Shugaban Ƙasa, Sisi ya rage ƙarfin Ƙungiyar ‘Yan Uwa Musulmi da kuma duk wani da ake zargin yana goyon bayan Ƙungiyar, wadda a halin yanzu Misra ta ce ƙungiyar ‘yan ta’adda ce.
An kama Morsi ne bayan juyin mulkin 2013, ya kuma fuskanci tuhuma a kan laifuka uku da suka haɗa da kwarmata bayanan sirri na Gwamnatin Misra ga Qatar, kashe masu zanga-zanga lokacin da aka yi zanga-zangar yin zaman dirshan a wajen Fadar Shugaban Ƙasa da kuma yi wa Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa leƙen asiri.
An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai sakamakon yi wa Qatar leƙen asiri, da kuma hukuncin zama gidan yari na shekara 20 sakamakon kashe masu zanga-zanga. An dakatar da wani hukuncin kisa da aka so a yanke masa sakamakon buɗe gidan yari lokacin da aka yi juyin mulkin a wata ƙara da aka yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2016.
Tsohon Shugaban Ƙasar, wanda ke da tarihin rashin lafiya, da ya haɗa da cutar sanyi, hanta da ƙoda, an ajiye shi a cikin kaɗaici a Gidan Kaso na Tora dake Alƙahira.
A 2018, wani gungun ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya su uku suka bada rahoton cewa akan ajiye Morsi cikin kaɗaici tsawon sa’o’i 23 a yini, inda ake ba shi awa ɗaya kawai don ya motsa jiki. ‘Yan Majalisar, waɗanda Crispin Blunt ya jagoranta, sun ce yadda ake ajiye Morsi akwai azabtarwa, kuma zai iya kawo ƙarshen rayuwarsa.
“Mun yadda da ra’ayin cewa rashin kyakkyawar kulawa da ba ya samu zai iya kasancewa abinda ya haifar da taɓarɓarwar halin da yake ciki, abinda kuma zai iya kawo mutuwarsa da wuri”, in ji ‘yan Majalisun.