Kotun Ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin ɗan takarar gwamna na PDP a Kano

149

A ranar Talata ne Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da ɗaya daga cikin waɗanda suka so jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar gwamna a Jihar Kano, Ibrahim Little ya shigar gabanta, inda yake ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDPn.
Kotun Ƙolin ta ce ta yi watsi da ƙarar ne sakamakon rashin shigar da ƙarar yadda ya kamata.

A ranar 18 ga watan Afrilu, Wata Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zamanta a Kaduna ta tabbatar da Abba a matsayin ɗan takarar gwamna a PDP, bayan ya shigar da ƙara gabanta inda yake ƙalubalantar hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya dake Kano, wadda ta ce bai cancanta ya yi takarar ba.

Da yake gabatar da hukuncin, Mai Shari’a Tanko Hussaini ya ce alƙalin Babbar Kotun Tarayya dake Kano ya yi kuskure a sharia’ance, inda ya yi zaton yana da hurumin yanke hukunci ba tare da mai shigar da ƙara, Ibrahim Little ya sa Abba Kabir Yusuf a ƙarar ba.

Alƙalin ya ce Mista Little ba shi da ikon shigar da ƙara a zaɓen da bai shiga an yi da shi ba.

A ranar 4 ga watan Maris, wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta ce ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf bai cancanta ba.

Alƙalin Kotun mai lamba 1, Lewis Allagoa, ya yanke hukuncin cewa jam’iyyar PDP ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na ‘yan takarar gwamna ba a jihar.

Mista Little ya tunkari Kotun Ƙolin ne inda yake ƙalubalantar nasarar Mista Yusuf a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Kano, yana mai cewa Mista Yusuf ɗin ya yi nasarar zama ɗan takarar ne ta haramtacciyar hanya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan