Martani: Manajan Gidan Zoo Na Kano Ya Yi Magana AKan Kudi Miliyan Bakwai Da Gwaggo Biri Ya Hadiye

245


Manaja mai kula da gidan Zoo na jihar Kano ya yi magana game da labarin batan kudi har naira miliyan bakwai da aka ce gwaggon biri ya hadiye.

Babban manaja mai kula da gidan Zoo, malam Umar Yusuf umar ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, hasalima barayi ne suka shiga suka yi musu sata ba biri ba.

A lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Guardian, malam Umar ya ce a ranar lahadi, tara ga watan Yunin Shekarar nan, shugaban masu tsaron gidan ya kira shi cikin dare, inda ya shaida masa cewa yan fashi sun shigan musu kuma sun sace kudi.

Ya kara da cewa, da misalin 6:30 na safe, sai ya garzaya zuwa gidan Zoo inda ya tarar da ofisoshin su a bankade, kuma ba tare da yin kasa a gwiwa ba ya gaggauta kiran DPO na Sharada Police Station.

Malam Umar ya bayyana cewa, shi bai taba zaton gaggwon Biri ne ya aikata hakan ba, illa ya aiyyana a ransa cewa wannan aikin barayi ne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan