Yara a Jihar Gombe sun yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta kare musu muradunsu

142

Majalisar Yara ta Jihar Gombe ta yi kira ga Gwamnatin Jihar da masu ruwa da tsaki da su ƙara himma wajen kyautata rayuwarsu da magance matsalolin da suke addabar su musamman ta fannin ilimi da lafiya da cin zarafi da ma kare musu ‘yanci da haƙƙoƙi.

Yaran sun yi kiran haka ne ranar Litinin ɗin nan yayin Bikin Alamta Ranar Yara ta ‘Yan Afirka, wadda Ƙungiyar Ceto Yara ta Save the Children ta shirya a Ɗakin Taro na Kwalejin Nazarin Aikin Jinya da Ungozoma ta Jiha, mai taken “Ayyukan jJn Ƙai a Afirka: ‘Yancin Yara Farko”.

Majalisar Yaran ta buƙaci gwamnati, da ta samar da manufofi da tsare-tsaren da za su taimaka wajen magance matsalolin yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da yin kira ga iyaye da su himmatu wajen sanya ‘ya’yansu a makaranta.

A nasa tsokacin, Daraktan Ƙungiyar ta Save the Children na Ƙasa ta bakin Shugabar ƙungiyar ta Jihar Gombe, Altine Lewi, ya bayyana ranar a matsayin wata dama ga yaran Nahiyar Afirka, wajen miƙa koke da buƙatunsu ga gwamnati da masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga yaran da su kasance wakilan miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin kasar nan.

“Ku yi amfani da wannar dama wajen isar da buƙatun abokai da ‘yan uwanku da ba su samu damar shiga makaranta ba wajen ganin an ceto su daga wannan hali tare da ba su haƙƙoƙinsu na samun ilimi dai-dai da kowa”, a cewar Daraktan.

Wassu daga cikin mahalarta taron sun buƙaci Gwamnatin Jihar da ta ɗabbaƙa Dokar ‘Yancin Yara don kare su daga cin zarafi da kare musu haƙƙoƙi.

Wakilan Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu da hukumomin gwamnati, sun bayyana irin shirye-shiryen da na kyautata rayuwar yara.

Daga Yunusa Isa Kumo

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan