Buhari ya sauke Manajan Daraktan NNPC

140

Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Mele Kolo Kyari a matsayina sabon Babban Manajan Daraktan (GMD) Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC.

Wata sanarwa da Janar Manaja na Gungun Kamfanonin NNPC, Jami’in Hudɗa da Jama’a, Ndu Ughamadu ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta ce haka kuma Shugaba Buhari ya naɗa sabbin Jami’an Gudanar da Aiki bakwai tare da Kyari.

Har lokacin naɗin nasa, Kyari, wanda masanin ilimin ƙarƙashin ƙasa ne, shi ne Janar Manaja na Sashin Sayar da Ɗanyan Man Fetur na NNPC, kuma a lokaci guda, shi ne Wakilin Najeriya na Ƙasa a Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur, tun daga 13 ga watan Mayu, 2018.

Shugaba Buhari ya umarci sabon GMD ɗin da sabbin Manyan Jami’an Gudanar da Aikin da su yi aiki da waɗanda ke riƙe da ofisoshin daban-daban har zuwa 7 ga watan Yuli, 2019 don miƙa mulki yadda ya kamata ranar 8 ga watan Yuli, 2019, lokacin da naɗin nasu zai fara aiki.

Amma naɗin Farouk Garba Said (Arewa Maso Yamma), wanda zai maye gurbin wani Babban Jami’in Gudanar da Aiki zai fara aiki ne ranar 28 ga watan Yuni, 2019.

Manyan Jami’an Gudanar da Aikin su ne:
Roland Onoriode Ewubare (Kudu Maso Gudu) – Babban Jami’in Gudanar da Aiki, Haƙo Man Fetur

Injiniya Mustapha Yinusa Yakubu (Arewa ta Tsakiya) –Babban Jami’in Gudanar da Aiki Tacewa da Arbakatun Man Fetur

Injiniya Yusuf Usman (Arewa Maso Gabas) – Babban Jami’in Gudanar da Aiki, Iskar Gas da Wutar Lantarki
Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu (Kudu Maso Gabas), Babban Jami’in Gudanar da Aiki, Sashin Kasuwanci

Injiniya Adeyemi Adetunji (Kudu Maso Yamma) – Babban Jami’in Gudanar da Aik, Downstream

Farouk Garba Said (North West) – Babban Jami’in Gudanar da Aiki Corporate Services.

Ughamadu ya bayyana a cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai cewa Manajan Daraktan NNPC, Dakta Maikanti Baru ya taya sabbin waɗanda aka naɗa ɗin murna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan