Turkashi: NDLEA Ta Kama Mutum 83,058 Akan Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi

154

Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) ta ce ta kama mutum dubu 83, 058 akan zargin sha, da laifukan ta’ammali da Miyagun kwayoyi, tare da gurfanar da kararraki guda dubu16,937 a gaban shari’a a tsawon shekaru Goma.

Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta Col Muhammad Mustapha Abdullahi mai ritaya a yau alhamis 20 ga watan Yuni shekarar 2019 a garin Abuja yayin kaddamar da shirye-shiryen bikin ranar yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da fataucin su da za a yi a ranar 26 ga watan nan.

Shugaban hukumar, wanda ya samu wakilcin Barrister Femi Oloruntoba ya bayyanacewa bikin na bana yana dauke da taken Lafiya don adalci: Adalci don lafiya, wata dama ce da kasarnan zata yi amfani da ita wajen amsa tambayoyi kan hanyoyin magance matsalolin miyagun kwayoyi da gwamnati tare da masu ruwa da tsaki suke bi da sauransu.

Barrister Femi ya bayyana takaicinsa bisa yadda bincike ya nuna cewa a bare an samu mutum miliyan 14.3 masu shekaru 15 zuwa 64 da suka yi ta’ammali da miyagun kwayoyi. Hakan ya nuna cewa an samu karin yawan mutane masu ta’ammali da miyagun kwayoyin fiye da shekarun baya.

A karshe, Barrister Femi ya ce, wannan yasa hukumar ta canza tsarinta daga yin biki a ranar 26 ga watan Yunin kowacce shekara zuwa gudanar da shirye-shirye gangamin wayar da kai, tare da ilimantar da al’umma illar shaye-shaye a garin Abuja da sauran ofisoshin su na jihohi a fadin kasar nan har na tsawon kwanaki shidda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan