Manoma a Gombe sun koka bisa rashin raba taki da wuri

56

Wasu manoma a Gombe sun koka game da gazawar gwamnati wajen raba takin zamani da sauran kayan aikin gona da wuri a jihar.

Manoman, waɗanda suka yi magana a tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Gombe ranar Juma’a sun ce raba kayan a makare zai shafi noman bana.

Sun je jinkirin zai kuma iya shafar amfanin gonarsu saboda ba a zuba takin zamani a lokacin da ya dace ba.

Nafada Suleiman, wani manomin masara ya ce jinkirin ya zama wani abu da ake samu duk shekara, sakamakon jerin wahalhalun da manoma ke fuskanta kafin su samu takin.

Ya ce jinkirin yana kashe wa manoma da yawa guiwa wajen ci gaba da noma.

Yusuf Andrew, wani manomin shinkafa ya ce duk da saukar damina, takin zamani da za a yi aiki da shi don neman wuri bai samu a kan lokaci ba, “abinda babu shakka zai shafi amfanin gona”.

Ya yi kira ga gwamnati da ta yi gaggawa wajen maganin matsalar rashin isasshen amfanin gona.

“Yanzu a wasu sassan jihar nan, mun fara samun ruwan sama, amma har yanzu ba a samu takin zamani wanda za mu taimaki manoman da ba su da isassun kuɗin da za su siya ba.

“Noma yana yin tsada saboda ƙarancin gonaki, kuma ba tare da zuba isasshen takin zamani ba, kamar maganin ƙwari da sinadaran aikin gona, waɗanda ke da tsada sosai, kuma manoma su kaɗai ba za su iya siyan waɗannan abubuwa masu tsada ba”, in ji shi.

Andrew ya yi kira da a yi bitar tsarin yadda ake raba takin zamani a jihar don bunƙasa aikin gona.

“Wannan ya zama wajibi saboda aikin gona shi ne sana’ar da ta mamaye yankin nan, inda kimanin kaso 80 cikin ɗari na al’ummar yankin ke yin noma don kasuwanci da kuma ciyar da kai.

Hajiya Zainab Mohammad, wata mai noman auduga ta jaddada buƙatar da ake da ita na raba kayan aikin gona da wuri don jan hankalin matasa su shiga aikin gona.

Hajiya Zainab ta yaba wa Babban Bankin Najeriya, CBN bisa shirinsa na tallafa wa manoma mai suna Anchor Borrower’s Programme, ABP, da yadda ya yi tsari mai kyau wajen raba kayan aikin gona da wuri ga manoman auduga daga ƙananan hukumomi bakwai inda ake noman auduga don kasuwanci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa a ranar Litinin ne Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya ƙaddamar da Kwamitin Kar-ta-kwanan mai mambobi bakwai wanda zai kula da yadda za a raba takin zamani, wanda Maina Binus, Jami’in Shirin Bunƙasa Aikin Gona na Jihar Gombe zai jagoranta.

Lokacin da wakilin jaridar WikkiTimes ya tunkari Binus don jin ta bakinsa bai ce komai ba.

Amma wata babbar majiya a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Gombe ta tabbatar wa NAN cewa Ma’aikatar ta fara samun takin zamanin da gwamnatin mai ci ta siyo.

Majiyar ta kuma bayyana cewa nan da mako biyu masu zuwa za a fara rabawa tare da siyar da takin ga manoma.

“Gwamna yana da sha’awar aikin gona sosai, kuma yana ɗaukar batutuwan aikin gona da gaske”, in ji Binus.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan