Batun Gayyatar Iyalan Marigayi Dr. Ado Bayero -Ba’a Yiwa Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado Adalci ba

213

Tun jiya na ji ana ta cece-ku-ce a gidajen Rediyo, musamman a Kano kan wata wasika da Shugaban Hukumar Sauraren Korafe-Korafe Kan Cion Hanci da rashawa Muhuyi Magaji Rmin Gado ya rubuta.

Ita dai wasikar tana gayyatar wadansu dattawan masarautar Kano ne, da wadansu iyalan Marigayi Mai Martaba Alhaji Dakta Bayero, su je su yi wadansu bayanai.


Sai dai kafin na cigaba, bari na tuna mana fadin Allah (SWT) da ya ce, ‘’Idan za ka yi Hukunci a Tsakanin Mutane, ka yi da gaskiya, ka da ka karkata’’.


Jim kadan bayan fito da wancan wasikar. Ya bude fage ga ýan siyasa da kuma wadansu Ýan Jarida wadanda suke daukar matsaya wani bangare. Ma fi yawansu, sun karkata ne ga bangaren Gidan Sarauta’watakila ko domin kauna, ko kuma wani abu da za a ba su.


Yawancin kalaman Yan siyasa da Ýan jaridar da ba sa jin kowane bangare; ko kuma idan sun ji su kawar da kai shi ne:


‘’Muhuyi Magaji ya wuce gona da iri’’. ‘’Muhuyi Magaji yana aiki da umarnin Ganduje’’


‘’Muhuyi Magaji ya sha ta karfin bakinsa’’


‘’Muhuyi Magaji ya yi amai ya lashe’’Akwai ma wani Dan Jarida da ke cewa ai Gwamna Ganduje ya bawa Biri ashana. Idan ba a kwace ba, zai iya kona dukkanin dajin.


Babban rashin adalcin da aka yiwa wannan bawan Allah shi ne; cikin masu dira kansa game da batun gayyatar dattawan Masarautar Kano da iyalan marigayi Dakta Ado Bayero shi ne, babu wanda ke tsayawa ya fadi dalilan da Muhuyin ya bada na gayyatarsu ba, sannan kuma babu wanda ya damu ya yi nazarin takardar janye wancan gayyata da Muhuyi ya rubuta, saboda rashin adalci.


Ba sai na kawo takardar gayyatar ta su ba, domin daya wacce Muhuyi ya janye gayyatar tana fassara wasikar farko ce ta gayyatar. Muhuyi Magaji ya ce:


‘’Ina so a sani, wallahi sam wannan Hukuma ba ta san ko su wanene wadancan mutane wadanda muke gayyata ba. Mu dai muna aiki ne da takardun da muke da su a hannu na tafiya neman magani wadda babu wani sunan Asibiti a Najeriya da ya tura wadannan mutane.


A saboda haka ne, muka yi zargin watakila babu wasu kudin magani ko tafiya neman magani. Sai muka zargi an dai fake da batun magani ne aka salwantar da kudin. Domin ita masarauta ta ki ta ba mu hadin kai akan wannan bincike. Don haka dole komai ya dagule.


Yanzu mun janye batun gayyata, Amma a karkashin dokar wannan Hukuma ta 2008, sashe na 31, muna bukatar Masarautar Kano su gabatar mana da wadannan takardu don Allah.


1. Dukkanin takardu muhimmai wadanda za su yi bayani kan wadannan mutane wadanda aka ce an kashe wadannan kudade domin su wajen neman magani.
2. Kuma muna bukatar dukkanin takardun wadancan Asibitoci na karba da kwanciya da za su tabbatar da ikirarin hakan.


Hakan hakika zai taimakawa wannan Hukuma.
DON ALLAH MENENE LAIFIN MUHUYI ANAN?


Ni a gani na, Muhuyi ba shi da wani laifi. Domin ya yi gayyatar ne saboda masarautar Kano ta ki ba shi hadin kai. Na tabbata, da ita masarautar tana fito da komai dalla-dalla, watakila da yanzu an wuce wurin. Ina da tabbaci, da a ce Muhuyi ya san wadancan dattijai su ake nufi, to zai san yadda zai fuskanci abin.

KIRA GA GWAMNA GANDUJE, IDAN SUKA TUNZURA KA, HAR KA CIRE MUHUYI MAGAJI, TO KA KASHE DARAJAR WANNAN HUKUMA.


Anan ina tunawa da lokacin Gwamnatin Malam Dakta Ibrahim Shekarau. Ya saka Malam Rabo a matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai na Jihar Kano.


Malam Rabo ya saka rigar da babu wuya da masu keta dokokin Jihar Kano da Hukumar.
Aka yi ta zaginsa da yi masa hujumi iri-iri. Amma ya tsaya kyam akan aikinsa tsakani da Allah. Shi kuma Malam Ibrahim Shekarau ya kawar da kai daga sukar Ýan siyasa da jamaá, ya kyale Rabo yayi aikinsa.


Babban abin da aka girba shi ne, Hukumar ta rike mutuncinta, kuma ta saita masu harkar fina-finai, sannan har yanzu wannan gini da Rabo ya yi mata da goyon bayan Malam Shekarau, ita Hukumar ke girba.


A domin haka, ya kamata Gwamna Ganduje ya kyale Muhuyi ya cigaba da aikinsa kamar yadda doka ta tanada. Idan kuwa har ya karkata ga matsin lambar wadansu mutane, to shi kenan, wannan Hukuma za ta tashi daga aiki.


A duk lokacin da aka soma wani babban bincike, ýan siyasa da wadanda abin bai musu dadi ba, sai su yi ca. Daga nan sai a janye.
Muhuyi Magaji, cigaba da aikinka, ciki da gaskiya wuka bata huda shi.


(Daga Baballe Saye)


Za ku sake ji na nan gaba kadan da yardar Allah.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan