Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta buƙaci Turawan Zaɓenta, EOs da su bayyana ra’ayoyinsu da suka a kan yadda aka gudanar da babban zaɓen 2019, tana mai cewa ba zaɓen da yake cikakke.
Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana haka a Taron Bitar Zaɓen 2019 da Turawan Zaɓe daga jihohi 19 ranar Litinin a Abuja.
Farfesa Yakubu ya ce Hukumar a shirye take ta karɓi suka game da zaɓukan daga masu ruwa da tsaki, musamman EOs waɗanda ba wai kawai mambobin Hukumar ba ne, amma sun shiga an gudanar da zaɓen da su.
Ya bayyana cewa suka game da zaɓukan zai taimaka wajen inganta tsarin zaɓen ƙasar nan.
“Don Alla, kar ku ji tsoron ba Hukumar shawara. Inda muke buƙatar a soke mu, ko mu soki kanmu, don Alla ku yi haka.
“Na kan nanata cewa abokai za su soke ka, amma abokan gabarka za su yi Alla-wadai da kai. Amma suka ita ce tushen dake sa kowane tsari ya yi aiki.
“Ba wata dimukoraɗiyya, ba wani tsarin zaɓe da yake cikakke. Kowace dimukoraɗiyya ana tafiya ne ana ci gaba.
“Saboda haka, kar ku ji tsoro ku bada shawara kan dukkan batutuwan da suke da dangantaka da zaɓe, gaba ɗaya.
“Kuma, kuna da kariyar Shugaba, cewa duk abinda kuka ce ba za a zarge ku ba”, in ji shi.
Farfesa Yakubu ya yabi EOs ɗin bisa irin gudummawar da suka bayar wajen sauke nauyin da Hukumar ta ɗora musu.
Waɗannan abubuwa, a cewarsa, sun haɗa da yi wa masu zaɓe rijista, kula da harkokin jam’iyyun siyasa da gudanar da zaɓuka.
“Shirye-shiryen manyan zaɓuka, kai ma’aikata wuraren aiki, buɗe Tashoshin Zaɓe, PUs, tsara aikace-aikacen Tashoshin Zaɓe ranar zaɓe, duba shirye-shirye, dukkan waɗannan aikace-aikace ne da suke kacokan a kan EOs.
“Duk wani abu da wani zai faɗa game da gudanar da zaɓuka a Najeriya ne na biyu ne ga irin bayanan da za mu ji daga waɗanda suka gudanar da zaɓe a dukkan matakai- shi ne abinda ke da muhimmanci- tashoshin zaɓe”, in ji Farfesan.
A tsokacinsa, Dokta Mustafa Lecky, Kwamishinan Ƙasa na INEC, kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsare, Sa ido da Dabaru, ya ce manufar bitar shi ne a duba yadda aka gudanar da zaɓen 2019 a kuma koyi darussa.
Lecky ya ce bitar za ta ba Hukumar damar duba manufofi da shirye-shiryenta a zaɓen da ya gabata, wanda hakan zai zama wani kadarko wajen gudanar da zaɓukan 2023.
“Wannan wata hanya ce ta yin nazari SWOT, da ya haɗa da gano ƙarfinmu, hazaƙarmu, rauninmu ko matsaloli, damammakin da muka amfana da su ko muka rasa.
“Wannan ya kuma haɗa da matsaloli, barazana da suke a kan dukkan tsare-tsaren kafin, lokacin da bayan zaɓukan 2019.
“Wannan ya haɗa daga shiri zuwa aiwatarwa, har zuwa bayan kammalawa, saboda haka jadawalin bitar da tsarin aikace-aikace ya samar da tuntuɓa a dukkan matakai”, in ji Lecky.
Kwamishinan Ƙasar ya ce tsarin bitar ya game batutuwa bakwai da suka haɗa da Cibiyoyin Yankunan Rijista, shirye-shiryen zuwa ranar zaɓe.
Shugaban Shirin European Union Support to Democratic Governance in Nigeria, Maria Mauro ya siffanta EOs a matsayin ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki mafiya muhimmanci a zaɓuka.
Mauro ya yabi INEC bisa yadda ta dage wajen biyar zaɓukan 2019, yana mai ƙarawa da cewa tsarin bitar da Hukumar ke aiki da shi zai bada kyakkyawan sakamako wajen inganta tsarin zaɓe a Najeriya.