A ranar Litinin ne da yamma Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire, JAMB ta yi holi da wani mai suna Adah Eche, wani mai neman gurbin karatu ɗan shekara 19, wanda ake zargin ya kawo sakamakon ƙarya na Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire da aka fi sani da UTME.
Farfesa Is-haq Oloyede, Magatakardar JAMB ya yi holin wanda ake zargin a gaban manema labarai a Hedkwatar Hukumar dake Bwari, a Birnin Tarayya, Abuja.
Farfesa Oloyede ya ce wanda ake zargin ya zana Jarrabawar UTME ta 2019, ya samu maki 153, amma sai ya haɗa kai da wani mai maguɗin jarrabawa wanda ake zargin ya ƙara masa maki.
Ya yi bayanin cewa an cafke wanda ake zargin ne bayan wasu wakilan Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe Jama’a sun kai wa Hukumar ziyara bisa yawan ƙorafe-ƙorafe da wasu ɗalibai da suka zana Jarrabawar UTME ta 2019 ke yi.
Ya ce: “Sai muka zaɓi mutane uku daga cikin masu ƙorafin don warware musu matsalolinsu, kuma sai aka yi sa’a shi ne mutum na farko da muka zaɓa, kuma tabbas ya rubuto mana takardar ƙorafi, ya kuma sani sarai cewa ya yi ƙarya a sakamakonsa.
“Abinda muka yi shi ne mu gayyace shi don ya karɓi takardarsa ta samun gurbin karatu, kuma ya zo.
“Yanzu, abinda irin waɗannan mutanen ba su sani ba shi ne muna da lamba ta musamman a kowane sakamako, wadda take taimakon mu mu tantance sahihancinsa, amma wannan sakamakon na ƙarya yana da lamba ta musamman ta kasuwa, sai ta riƙa cewa lamba ta musamman ba daidai ba ce a shafinmu.
“Mun duba shafinmu, mun ga ya duba sakamakonsa har sau uku a jere ta hanyar 55019, kuma an ba shi amsa da sakamakonsa na ainihi, wanda shi ne 153, amma duk da haka ya dage kan cewa bai san sakamakon dake ɗauke da 290 na bogi ba ne”.
Farfesa Oloyede ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan an samu hujjoji da yawa daga wayarsa, da wasu a kwamfiyutarsa inda da farko ya sa wa kansa maki 200 na bogi, kafin ya ƙara shi zuwa 290.
Ya kuma ce sakamakon na bogi yana ɗauke da lamba 55019 a matsayin wanda ya turo sakamakon.
A cewarsa, an gano wasu ma’amaloli da wanda ake zargin ya yi a wani dandalin WhatsApp a kan wayarsa, inda ya karɓi kuɗaɗe daga hannun wasu mutane ya tura wa takwaransa don a ƙara makin UTME.
“Ya ce: “Ya karɓi kuɗi daga hannun wasu.
“Muna da huɗɗar da ya yi a wayarsa, inda wasu kan turo N5,000 suna neman taimako, su tura masa lambarsu ta rijista, adireshin Imel, da dukkan wasu bayanai da suka wajaba don ya taimaka ya ƙara musu maki.
“Waɗannan mutanen su ne dai suke kukan ƙarya, suna cewa ba su ga sakamakonsu ba, ko kuma ba su zauna jarrabawar ba, amma sun ci.
“Waɗannan mutane ba su san cewa mun kafa matakan tsaro dake taimakon mu wajen gano irin waɗannan abubuwa ba.
“Shi yasa muka dage kan cewa ɗalibai da suka fusata su zo wajenmu da hujjoji da takardu, kuma za mu warware wannan matsalar, amma sun ƙi.
Magatakardan ya ce shafin Intanet na Hukumar www.jamb.org, yana da wani dandali da mutane za su iya shigar da ƙorafinsu, kuma Hukumar tana aiki kullum don tabbatar da cewa ta saurari dukkan batutuwan da aka gabatar”.
Farfesa Oloyede ya ce: “Kawo yanzu, mun warware matsaloli 36,275 waɗanda aka samu daga dandalin, mun rufe 36,247, batutuwa 28 ne kawai suka rage mana ba mu warware ba har.
“Misali, yau kaɗai, mun samu ƙorafe-ƙorafe 143, daga ciki mun warware 118, 25 ne kawai ba a warware ba.
“Muna ci gaba da bada umarni cewa dole a miƙa dukkan ƙorafe-ƙorafe ta Intanet, kuma za mu warware waɗanda batutuwa kullum, amma mutane sun fi so su bi ta ɓarauniyar hanya”.
Farfesa Oloyode ya ce za a miƙa wanda ake zargin ga ‘yan sanda, kuma Hukumar za ta ci gaba da gano da cafke dukkan waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki.
Wanda ake zargin, Adah Eche wanda ya ce ya rubuta UTME ɗinsa ne a Veritas University Centre, Bwari, ya kuma ce wannan shi ne karon farko da ya rubuta jarrabawar.
A cewarsa, ba a fitar da sakamakonsa ba a kan lokaci, saboda haka sai ya yi rubutu a Facebook, cewa bai ga sakamakonsa ba, daga nan sai wani mai amfani da Facebook ya ce zai taimaka masa.
“Ban taɓa haɗuwa da mutumin ba, amma ya yi alƙawarin zai taimake ni in samu sakamakon, sai ya ce in tura masa N2,000, kuma na tura masa, sannan ya turo min da sakamakon ta WhatsApp.
“Bayan nan sai ya ce in tura masa N3,000 don ya kawo min sakamakon, amma bayan na tura, bai ƙara ɗaga kirana ba.
“Ya toshe ni a WhatsApp, bayan nan kuma lambarsa ta daina shiga.
“Ban san cewa sakamakon bogi ba ne.
“Ya kuma roƙe ni da in sanar da sauran mutane, su turo kuɗi don su ma ya taimake su ya ƙara musu maki.
“Shi yasa aka samu waɗancan ma’amaloli a can.
“Ban san cewa mutum zai iya rubuta jarrabawar fiye da sau ɗaya ba ko haka, da ban yi haka ba, da na yi amfani da 153 don samun gurbin karatu a makarantar kimiyya da fasaha, amma wancan mutumin shi ne ya ja ra’ayina.
“Shawarata ga sauran jama’a shi ne su daina irin waɗannan munanan ayyuka”.