Najeriya na fuskantar durƙushewar tattalin arziƙi- Sanusi

138

A ranar Talata Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa saura kaɗan bashi ya yi wa Najeriya katutu, biyo bayan manufofin tattalin arziƙi marasa amfani kamar saka tallafi a albarkatun man fetur da wutar lantarki.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriyar, CBN, wanda ya yi jawabi a taron Ƙara wa Juna Sani na Asusun Ƙasa Karo na 3 da Ofishin Akanta Janar na Ƙasa ya shirya da ake yi a Coronation Hall, Ɗakin Taro dake Gidan Gwamnatin Jihar Kano, ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya daina bada tallafin man fetur da wutar lantarki, indai ana so ƙasar nan ta daidaita.

A ta bakinsa: “Bashi ya yi wa ƙasar nan yawa, kuma sauran kaɗan ya yi mata katutu.

“Abinda ke faruwa shi ne Gwamnatin Tarayya tana biyan tallafin man fetur, tana biyan tallafin kuɗin wutar lantarki, kuma idan aka samu tashin a kuɗin ruwa, Gwamnatin Tarayya za ta biya.

“Abinda ya fi kasancewa barazana ga rayuwa fiye da tallafin man fetur shi ne dole mu sadaukar da ɓangaren Ilimi, laifiya da kayayyakin more rayuwa don mu samu man fetur mai arha?
“idan da gaske ne Shugaba Buhari yana yaƙi da cin hanci, ya kamata ya cire hatsarin da yake ɓangaren kuɗi, ya tsayar da bada tallafin man fetur, wanda abu ne kamar damfara”.

Sarki Sanusi ya nace kan cewa dole Shugaba Buhari ya faɗa wa ‘yan Najeriya gaskiya game da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki, ya kuma ɗauki mataki da wuri saboda ƙasar nan tana da tulin bashi a kanta.

Sarkin ya ce: “Tunda na zo nan, dole fa ku karɓi abinda na faɗa a nan.

“Idan kuma ba kwa son jin gaskiya, to kar ku ƙara gayyata ta.

“To bari mu yi magana game da halin da dukiyar al’ummar Najeriya ke ciki.

“Muna da wasu matakai masu wahala da dole mu ɗauka, kuma ya kamata mu fuskanci gaskiya.

“Mai Girma, Shugaban Ƙasa ya faɗa a jawabinsa na rantsuwa cewa gwamnatinsa za ta cire mutane 100 daga ƙangin talauci.

“Jawabi ne da aka yi maraba da shi sosai ba wai kawai a ƙasar nan ba, har ma a duniya gaba ɗaya.

“Yawan mutanen dake rayuwa da talauci a Najeriya yana da ban tsoro.

“Zuwa shekara ta 2050, kaso 85 cikin ɗari na waɗanda ke rayuwa cikin tsananin talauci za su kasance daga nahiyar Afrika.

“Kuma Najeriya da Jamhoriyar Dimukuraɗiyyar Kongo za su kasance a gaba.

“Kwana biyu da suka wuce, na karanta cewa kuɗin da gwamnati ke kashewa wajen biyan bashi daga kuɗaɗen shugarta ya kai kaso 70 cikin ɗari.

“Waɗannan alƙaluma ba ƙarya suke yi ba.

“Alƙaluman gwamnati ne.

“Ina karanta su a jaridu.

“Idan kana kashe kaso 70 cikin ɗari na kuɗaɗen shigarka wajen biyan bashi, to fa kana maleji ne da kaso 30 cikin ɗari.

“Kuma ka ci gaba da bada tallafi ga albarkatun man fetur, sannan kana kashe Naira Triliyan 1.5 duk shekara a kan tallafin man fetur!

“Sannan kuma, muna bada tallafi ga wutar lantarki.

“Kuma wataƙila sai ka ciyo bashi daga Kasuwar Kuɗi ko Babban Bankin Najeriya don ka biya bashin giɓin da yake a wutar lantarki.

“Ina kuɗin da za a biya albashi?

“Ina kuɗin da za a biya harkar ilimi?

“Ina sauran aikace-aikacen gwamnati?

Basaraken ya ce tsawon shekara 30, gwamnatocin baya suna da wannan shiri da ake kira tallafin man fetur, yana mai nanata cewa wannan shi ne lokacin da ya dace a tsayar da shi don ceto tattalin arziƙin ƙasar nan daga durƙushewa.

Da yake jawabi lokacin taron ƙara wa juna sanin, Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris ya lurar da cewa: “Maƙasudin taron ƙara wa juna sanin shi ne don a haɓɓaka yin adalci da yin abu a fili a dukkan sassan harkar kuɗi na gwamnati da na tsarin gudanarwa.

“Ana sa ran cewa mahalarta taron nan za su amince cewa yin adalci da yin abu a fili su ne manyan abubuwan da za a yaƙi rashin gaskiya a hada-hadar kuɗi, saboda haka, abubuwa da dole a sama su kafin a samu ci bunƙasar tattalin arziƙi da ci gaba”, a kalaman Akanta Janar ɗin.

Idris ya buƙaci mahalarta taron da su yi aiki tuƙuru wajen gano ƙalubalen da ake da su wajen yin adalci da yin abubuwa a fili a wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, da inganta hanyar samun kuɗi mai zaman kanta.

A jawabinsa, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cin hanci a matsayin abinda ya hana tattalin arziƙin ƙasar nan ci gaba.

Ya gargaɗi masu riƙe da muƙaman gwamnati da masu zaman kansu da su guje wa cin hanci, yana mai bayyana cewa ofishinsa ba ya yadda da cin hanci.

A jawabinsa, Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wanda Mataimakinsa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce Gwamnatin Jihar Kano ita ce ta farko wajen kafa Asusun Bai Ɗaya, TSA, a kokarinta na yaƙar cin hanci da zirarewar kuɗi.

A cewar Gwamna Ganduje, jihar tana da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci don yin maganin jami’an gwamnati masu halayyar cin hanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan