A daina ɗaukar malaman da ba su dace ba aikin koyarwa- Teach For Nigeria

A ranar Alhamis ne Shugabar Ƙungiyar Teach For Nigeria, wata ƙungiya da ba ta kuɗi ba, Folawe Omikunle ta ce akwai buƙatar ɓangaren Ilimin ƙasar nan ya ɗauki mutane masu nagarta kuma mafiya kyau a matsayin malamai.

Misis Omikunle ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a wata tattaunawa a Legas cewa akwai buƙatar gwamnati ta fuskanci ta kuma canza yadda take ɗaukar malamai don ɗaukar mutane mafiya dacewa a tsarin koyarwa.

Ta ce mutane da yawa sun shiga harkar koyarwa ne don su rayu, ba wai don suna son koyarwar ba.

Ta ce akwai ƙarancin zaburarwa da rashin sha’awa a tsakanin wasu mutane dake sana’ar koyarwa.

“Akwai buƙatar da farko ma mu dubi yadda muke ɗaukar malamai.

“Akwai buƙatar mu duba mu gani ko muna ɗaukar malamai tare da ba su horon da ya dace don su yi nasara a aji.

“Ina jin inda ya kamata a fara shi ne yadda muke ɗaukar malamai.

“Su wa muke ɗauka? Mene ne dacewar mutanen da muke ɗauka? Mene ne haɗin? Mene ne ingancin ɗai-ɗaikun mutanen da muke ɗauka a matsayin malamai?

“A ƙasashen da suka ci gaba, yawancin mutane sukan bada misalin ƙasashe kamar Finland, Singapore da sauran ƙasashe da suke ƙwazo a ɓangaren Iliminsu.

“Sukan ɗauki mafiya dacewa, kuma mafiya ƙwazo a matsayin malamai.

“A ƙasashe da dama, mafiya dacewa kuma mafiya ƙwazo su ne suke koyarwa, saboda suna sun samun matsayi mai kyau, kuma su ba ɗalibai horo waɗanda daga bisani za su sauya tattalin arziƙinsu”, in ji ta.

Misis Omikunle ta ce koyarwa ita ce zaɓi na biyu ko na uku ga wasu mutane, yayinda wasu ke yin amfani a matsayin aikin yi na wucin gadi kafin su samu wata dama mai kyau.

Ta ce akwai buƙatar a mayar da aikin koyarwa wani abin alfahari, inda za a dinga ɗaukar mafiya dacewa kuma masu hakzaƙa.

“Muna da mutanen da suka shiga koyawa, saboda shi kaɗai ne kwas ɗin da aka ba su lokacin da suka nemi gurbin karatu.

Ta ce a Najeriya bankuna, kamfanonin man fetur da gas su ne ke ɗaukar mutane mafiya dacewa.

“Kowa yana son yin aiki a banki, asibiti, kamfanonin man fetur da na gas, amma ba wanda yake son ya yi aiki a matsayin malami.

“Na yi bincikena a wasu kwalejojin ilimi kuma na gano cewa, kaso ɗaya cikin ɗari na cikin ɗalibai dake Tsangayar Koyarwa ne suka zaɓi su zama malami.

“Ina jin muna cikin halin dokar ta-ɓaci, kuma abinda ya kamata a yi shi ne buƙatar gaggawa ta sauya ƙasarmu ta hanyar ilimi.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan