Home / Gwamnati / Ganduje ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati

Ganduje ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati

Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa tsohon Kwamishinan Muhalli, Ali Makoɗa a matsayin Shugaban Ma’aikata.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya sanya wa hannu ranar Alhamis a Kano.

Gwamnan ya taya sabon wanda aka naɗa ɗin murna, ya kuma yi kira gare shi da ya sadaukar da kansa wajen yi wa al’umma hidima.

Gwamna Ganduje ya yaba da da irin gudummawar da Makoɗa ke bayarwa wajen ci gaban jihar nan, ya kuma ƙara yaba masa bisa irin nasarorin da ya samu a wa’adin shugabancinsa na farko.

“Koyaushe Ali Makoɗa kadara ne a jiharmu. Saboda haka akwai buƙatar in tafi da kai shi a wa’adin mulkina na biyu”, in ji Gwamnan.

Mista Makoɗa yana da Digiri a Nazarin Ɗakin Karatu da Kimiyyar Siyasa, Diploma Mai Zurfi a Harkar Gudanarwa da Digiri na Biyu a Nazarin Kasuwanci daga Jami’ar Bayero ta Kano.

About Hassan Hamza

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *