Yadda ya kamata jami’an gwamnati su dinga amfani da kafafen sada zumunta na zamani- Pantami

157

Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani ta Ƙasa, NITDA ta yi kira ga hukumomin gwamnati da su bi dokoki da ƙa’idojin amfani da kafafen sada zumunta na zamani sau da ƙafa.

Darakta Janar na Hukumar, Dokta Isa Pantami, wanda ya yi kiran ranar Alhamis a wata sanarwa da ya bayar a Abuja ya tunatar da cewa an rattaba wa ƙa’idojin hannu sun zama doka ne tun a watan Janairu, sun kuma samar da dokoki da hukumomin gwamnati za su yi amfani da su yayin amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

“NITDA za ta so ta jawo hankalin hukumomin Gwamnatin Tarayya wajen buƙatar da ake da ita na su yi biyayya sau da ƙafa da framework da ƙa’idojin amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

“An fitar da tushen dokar da ƙa’idojin ne da nufin samar da jagoranci wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani da aka tsara don inganta sadarwa, yin abu a fili, yadda za a yi amfani da ma’amala da mutane.

“Wannan ya zama wajibi saboda bisa ga yadda aikin sa ido da Hukumar ke yi ya gano yadda wasu jami’an gwamnati suke amfani da asusunsu na ƙashin kai wajen aikin gwamnati.

“Mun kuma ƙara lura da inda ake amfani da asusun aiki, wasu jami’an gwamnati, idan wa’adin shugabancinsu ya ƙare sukan ƙi bada irin waɗannan asusu.

“Waɗannan abubuwa ne da sun saɓa da tanadin tushen dokar da ƙa’idojin waɗanda suka buƙaci jami’an gwamnati da kada su yi amfani da asusun ƙashin kai wajen aikin gwamnati”, in ji Mista Pantami.

Ya ƙara bayyana cewa ana buƙatar jami’an gwamnati da su miƙa asusun kafafen sada zumunta na zamani na aiki, su kuma shugabanni masu ci su canza lambar sirri don kare bayanai.

Darakta Janar ɗin ya yi gargaɗin dukkan asusun sada zumunta na aiki da suke ƙarƙashin kulawar jami’an gwamnati to fa na gwamnati ne, kuma dole a miƙa su yadda ya kamata.

“saboda haka NITDA, tana shawarar jami’an gwamnati da su tabbatar da cewa sun yi biyayya ga tanadin wannan doka a cikin kwanaki 14 da bada wannan sanarwa don guje wa fuskantar hukunci”, in ji shi.

Ya bada shawarar cewa ya kamata jami’an gwamnati da sauran jama’a su saba wa kansu da ƙa’idojin NITDA da suke a shafinta na Intanet_www.nitda.gov.ng

Mista Pantami ya ƙara yin gargadin cewa “karya ƙa’idojin NITDA laifi ne babba da za a iya yin hukunci ta hanyar tara, zama gidan kaso ko duka biyun”.

NITDA Hukuma ce ta Gwamnatin Tarayya da aka kafa a watan Afrilu, 2001 don aiwatar da Manufar Najeriya ta Bunƙasa Fasahar Sadarwa, ta kuma lura da yadda ake amfani da Fasahar Sadarwa a ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan