JAMB za ta fara yi wa ɗalibai rijista da lambar NIN

35

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire, JAMB ta ce daga shekara ta 2020, ɗalibai za su riƙa yin rijista don zana Jarrabawar da take shiryawa da Lambarsu ta Shaidar Zama ɗan Ƙasa da aka fi sani da NIN don yin maganin yin rijista fiye da sau ɗaya.

Fabian Benjamin, Shugaban Sashin Yaɗa Labarai na JAMB ya bayyana haka a wani taron ƙara wa juna sani da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Ƙasa, NECO ta shirya wa manema labarai masu ɗaukar rahoton ilimi ranar Juma’ar nan a Keffi.

Benjamin, wanda ya yi jawabi a kan tofik mai taken: “Fahimtar Ɗaukar Rahoto a Ƙarni na 21”, ya ce za a samu ci gaban ne da haɗin guiwar Hukumar Bada Katin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIMC.

A cewarsa, gogewa ta nuna cewa maguɗin jarrabawa a jarrabawar da gwamnati ke shiryawa musamman Jarrabawar Bai-Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire, UTME yana farawa ne tun daga matakin yin rijista.

“Kwanaki huɗu da suka wuce, mun soke sakamakon ɗalibai huɗu saboda maguɗin jarrabawa da muka gano bayan kammala jarrabawar. Hukumar tana kan batun, kuma ta lashi takobi kuma tana da fasaha a ƙasa da za ta iya yin aiki da ita don yin maganin maguɗi a wajen rijista”.
Wani muhimmin ɓangare na dabarun yin rijista da Hukumar ta ɗauka shi ne a taƙaita lokacin yin rijistar”, in ji Mista Benjamin.

Ya ce daga yanzu rijistar za ta riƙa ɗaukar tsawon kwana 30 ne, maimakon lokaci mai tsawo don hana ‘yan damfara ɓata tsarin rijistar.

Mista Benjamin ya kuma yi kira ga iyaye da su daina ƙarfafa wa ‘ya’yansu guiwar yin mguɗi.

Game da ƙalubalen ɗaukar hoton ɗan yatsa, ya ce Hukumar ta yi shirin kawar da matsalolin ɗaukar hoton ɗan yatsa daga nan zuwa shekara ta 2020.

“A 2018, mun samu matsalolin ɗaukar hoton ɗan yatsa har 24,490, amma mun iya rage wannan matsala zuwa 22 a 2019; amma idan mun iya cimma abinda muka tsara, zuwa 2020 ba za mu wata matsala ta ɗaukar hoton ɗan yatsa ba” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ba wata Cibiyar Ɗaukar Jarrabawar da ake yi ta Kwamfiyuta, CBT da Hukumar za ta yi amfani da ita wajen gudanar da jarrabawarta idan ba cibiyoyin da masu kula da cibiyoyin suka mallaka ba.

Da yake jawabi game da matsalolin yin sojan-gona a jarrabawar, Mista Benjamin ya ce idan ba a yi maganin yin rijista fiye da sau ɗaya ba, ita ce hanya mafi sauƙi ta yin sojan-gona.

Ya ce Hukumar za ta ci gaba da ba mutane masu buƙata ta musamman kulawar da ta dace.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan