Abinda Gwamnatin Tarayya ke nufi da kafa Ruga- Garba Shehu

119
Portraits from a Fulani marriage ceremony. Kajuru, North-western Nigeria.

Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin jin daɗinta bisa ce-ce-ku-cen da ake ta yi bisa shirinta na kafa Ruga don kawo ƙarshen rikicin da ake samu tsakanin Fulani da makiyaya.

Kafa Ruga yana nufin tsugunar da Fulani dake zirga-zirga.

A sauƙaƙe yana nufin wani matsuguni a karkara, inda makiyaya dabbobi, ba kawai masu kiwon shanu ba, za su zauna a wani waje mai tsari, tare da samar musu da kayayyakin more rayuwa.

Waɗannan kayayyakin more rayuwa sun haɗa da makarantu, asibitoci, hanyoyi, asbitin dabbobi, kasuwanni da kamfanonin da za su sarrafa su kuma ƙara wa nama kima da sauran albarkatun dabbobi.

Garba Shehu, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja ya yi bayanin cewa waɗanda za su amfana da Kafa Ruga sun haɗa da dukkan masu kiwon dabbobi, ba kawai Fulani makiyaya ba.

“Gwamnatin Tarayya tana shirya wannan ne don kawo ƙarshen kiwon dabbobi a fili, abinda ke kawo barazanar tsaro ga manoma da makiyaya.

“Amfanin wannan ga ƙasar nan ya haɗa da rage yawan rikici-rikice tsakanin makiyaya da manoma.

“Samun haɓakar samar da dabbobi, da tsarin amfani da zai ƙara inganci da lafiyar dabbobi ta fuskar samar da naman shanu da madara, ya ƙara ingancin ciyarwa da yadda za a kula da dabbobi, ya kuma bada dama ga kamfanoni masu zaman kansu su shigo ciki don samar da dabbobi ta hanyar zuba jari”, ya bayyana haka.

A cewar Mista Shehu, sauran alfanun tsarin sun haɗa da samar da ayyukan yi, damar samun bashi, samar da tsaro ga manoma masu zirga-zirga da kawo ƙarshen satar shanu.

Mista Shehu ya yi watsi da jita-jitar cewa Gwamnatin Tarayya za ta ƙwace filaye mallakin jihohi ko kuma ta tursasa gwamnatocin jihohi su karɓi shirin.

“A yi watsi da maganar siyasa da soki-burutsu da suka mamaye ra’ayoyi, babu wani shirin gwamnati na ƙwace filaye mallakin jihohi, ta yi mulkin mallaka ko ta ƙaƙaba Ruga ga kowane sashi na ƙasar nan.

“Gwamnati ta bayyana ƙarara ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba cewa shirin na sa-kai ne”, in ji shi.

Mista Shehu ya ƙara bayyana cewa kawo yanzu, jihohi 12 sun gabatar da buƙatarsu ga Ma’aikatar Aikin Gona ta Ƙasa, suna masu bayyana cewa za su samar da filayen da za a fara aiwatar da wannan tsari a jihohinsu, yana mai ƙarawa da cewa yawan jihohin zai isa a fara aiwatar da shirin na gwaji.

“Abin kaico, wasu gwamnatocin jihohi da ba su nuna sha’awarsu da shirin ba, kuma ba sa kan jerin sunayen waɗanda za a gayyata suna ta rikitar da mutane cewa Gwamnatin Tarayya tana shirin fara aiwatar da wani shiri don ta ƙwace musu filayensu.

”Yawanci, waɗannan shugabannin jihohi ne waɗanda ba su da bayanin da za su yi wa al’ummarsu bisa ci gaba da ƙin biyan albashin ma’aikata.

“Gaskiya ne cewa Gwamnatin Tsakiya ta tattara filaye a dukkan jihohin ƙasar nan, amma saboda ba wata manufa ta tursasa wannan shiri a kan kowa, gwamnati za ta taƙaita fara aiwatar da shirin ga jihohin 12 masu buƙata”, a kalaman Mista Shehu.

Daga nan sai Mista Shehu ya yi kira ga jihohi da su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen ƙarfafa gwiwar dukkan ɓangarorin dake ja-in-ja da wannan shiri da su yi ƙoƙarin kawo sulhu.

“Yayinda muke neman mafita ta din-din-din ga waɗannan rikici-rikice, dole a yi ƙoƙarin tabbatar da cewa ba wani mutum da za a muzguna wa ko a take masa haƙƙi da ‘yanci a ƙarƙashin dokokinmu”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan