Ana ci gaba da alhinin rasuwar Umar Sa’idu Tudun Wada

136

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masu Tace Labarai ta Ƙasa, NGE, Umar Saidu Tudun Wada ya rasu.

Gogaggen ɗan jaridar ya rasu ne jiya a wani haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa Kano daga Abuja.

Umar Sa’idu shi ne tsohon Manajan Darakta na Gidan Rediyon Kano, kuma ya taɓa zama Babban Edita na Gidan Talabijin na Jihar Kano, CTV, wanda ake kira Gidan Talabijin na Abubakar Rimi, ARTV a yanzu.

Tuni Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa game da rasuwar ta Mista Tudun Wada.

A wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman Kan Yaɗa Labarai, Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja, Shugaban ya siffanta marigayi Tudun Wada a matsayin kamilin mutum, kuma gogaggen ɗan jarida wanda ya kiyaye ƙa’idojin aikin jarida.

“Aikin jarida yi wa al’umma hidima ne, saboda shi ne tabarau da al’umma ke yin amfani da shi wajen kula da abubuwan da shugabanni ke yi. Ina mai alfaharin cewa marigayi Tudun Wada ya taka rawarsa yadda ya dace.

“Bari in yi amfani da wannan dama in miƙa saƙon taaziyyata ga Ƙungiyar Masu Tace Labarai, Gwamnatin Jihar Kano da iyalan Tudun Wada. Allah Ya ba su haƙurin jure rashin, Ya kuma saka wa marigayin da Aljannar Firdausi”, in ji sanarwar.

Haka kuma, a jiya NGE ta yi alhinin rasuwar ta Mista Tudun Wada, wanda suke kira UST.

A wata sanarwa da Shugabanta, Funke Egbemode da Sakatare Janar, Mary Atolagbe suka fitar, Ƙungiyar ta bayyana alhini da kaɗuwarta bisa rasuwar Umar Sa’idu Tudun Wada.

“Mutuwarsa kwatsam biyo bayan wani mummunan haɗarin mota ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni a kusa da garin Kura a Ƙaramar Hukumar Kura dake Jihar Kano ta bar mu mun kasa cewa komai.

“Koda yake, a kowane irin hali, dole mu tuna mu ci gaba da gode wa Alla Maɗaukakin Sarki, wanda ya fi kowa sani.

“Muna miƙa saƙon taaziyyarmu mai cike da soyayya da alhini ga iyalansa, waɗanda za su ji raɗaɗin rashinsa.

“Muna kuma miƙa jajenmu ga abokansa, abokan aiki da ma’aikata dake Gidan Rediyon Kano inda UST ya taɓa zama Manajan Darakta.

“Yadda ya zama Mataimakin Shugaban NGE ba tare da hamayya ba a taro na ƙarshe da aka yi a Legas ranar 4 ga watan Mayu, 2019 ya nuna yadda ake mutunta shi, girmama shi da irin gwaggwaɓar gudunmawarsa da yake ba Ƙungiyar.

“UST: Babu shakka za mu yi kewar ka. Mun yi ban-kwana da mutum na gari! Mun yi imani cewa Alla Ya fi mu son ka, kuma muna fata zai tanadar maka waje a Aljannar Firdausi”, saƙon taaziyyar Ƙungiyar ya bayyana haka.

Mista Tudun Wada shi ne tsohon Shugaban Gungun Gidajen Freedom Rediyo, Tashar FM mai zaman kanta irinta ta farko a Arewacin Najeriya. ya taɓa yin aiki da Muryar Amurka, wato Voice of America, VOA, ya kuma yi aiki da Sashin Hausa na Deutsche-Welle, ya kuma taɓa zama Editan Concern Magazine.

Ya taɓa zama Mataimaki na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai ga tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso har sau biyu, ya kuma taɓa zama Sakataren Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa, Reshen Jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan