Buhari bai saki sabbin sunayen ministoci ba- Garba Shehu

138

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu, ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa Shugaba Buhari ya saki sunayen sabbin ministoci, har ma ya miƙa sunayen ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa don amincewa.

Mista Shehu ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Asusuna na Twitter ingantacce ne. Duk wanda yake son ya san abinda na faɗa sai ya tafi can, ba ga na bogi ba. Ba ni da wani labari mai ɗumi game da naɗa ministoci, saboda ba a yi min bayani game da hakan ba.

“Ku yi watsi da rahoton da suke dangantawa da ni, don Alla”, in ji Mista Shehu.

Labarai24 tana neman afuwar masu karatu bisa kawo wancan labari mara inganci.
A yafe mu!

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan