Yadda jami’an tsaro suka kuɓutar da surukin dogarin Buhari

137

Jami’an tsaro a Kano sun kuɓutar da Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura wanda wasu masu garkuwa da mutane aka sace a gidansa dake kimanin watanni huɗu da suka gabata.

Malam Tukur Umar, ƙanin wanda aka sace ɗin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Talata cewa an kuɓutar da Magajin Garin Daura ne da misalin ƙarfe 7:25 na safiyar yau Talata.

Ya ce wani wani tim ɗin haɗin gwiwa na jami’an tsaro ne ya kuɓutar da Magajin Garin bayan an yi musayar wuta da waɗanda suka sace shin, waɗanda aka tsare shi a wani gida dake Titin Madobi a Unguwar Samegu, kusa da Cibiyar Matasa ta Sani Abacha dake Kano.

“An ceto shi lafiya lau, kowane lokaci daga yanzu zai iya kasancewa a Daura don a haɗa shi da iyalinsa. Mun gode Alla, Alla ya amsa addu’armu”, in ji Mista Umar.

Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa jajircewarsu, wadda ta sa aka iya tseratar da Hakimin, ya ce iyalinsa ba za su taɓa mantawa da su ba.

NAN ya ruwaito cewa a ranar 1 ga watan Maris, 2019 ne aka sace Musa-Uba, Magajin Garin Daura, mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari, kuma tun lokacin ba a ƙara samun tuntuɓa tsakanin iyalinsa da waɗanda suka yi garkuwa da shi ba.

Har yanzu Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ba ta bada wata sanarwa game da tseratar da Mista Uba ba.

Yunƙurin yin magana da Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar, Gambo Isa bai yi nasara ba, saboda layukan wayarsa ba sa shiga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan