Abinda yasa zan yi takarar gwamnan Kogi- Dino Melaye

165

Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai, Dino Melaye ya sayi fom don yin takarar gwamnan Jihar Kogi a zaɓen gwamna da za a gudanar a jihar watan Nuwamban wannan shekara.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ya karɓi fom ɗin nasa a Sakatariyar Jami’yyar PDP ta Ƙasa ranar Alhamis a Abuja, Mista Melaye ya sha alwashin kayar da Gwamna Yahaya Bello da jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

A cewarsa, zai sake gina tare da saita tattalin arziƙin jihar idan al’ummar jihar suka ba shi dama.

Ya ce shi ne mutumin da ya fi gogewa, kuma ya fi dacewa da ya zama gwamna, yana mai ƙarawa da cewa jam’iyyar PDP za ta kayar da jam’iyyar APC a jihar saboda Gwamnan Jihar, Yahaya Bello bai taɓuka komai ba.

Ya nuna rashin jin daɗi bisa halin tsaro, halin tattalin arziƙi, rashin biyan albashi da sauran matsalolin dake damun jihar, yana mai ƙarawa da cewa zai saita jihar idan har aka ba shi dama.

“Na zo nan ne don in saita Kogi, za mu dawo da fata da haɗin kai tsakanin al’ummar Jihar Kogi. Muna son al’ummarmu.

“Ba muradina ba ne, muradin al’umma ne. Gwamnan bai kammala aiki ko ɗaya ba a jihar. A shirye muke mu sake gina jihar nan”, in ji Mista Melaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan