An tsaurara tsaro a Osun gabanin hukuncin Kotun Ƙoli na gobe

158

A ranar Alhamis ɗin nan Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta ce ta tsaurara tsaro a jihar don hana karyewar doka da oda gabanin hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke ranar Juma’a game da zaɓen gwamnan jihar na 2018.

Mai magana da yawun Rundunar, DSP Folashade Odoro ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan sanda a shirye suke don jiran sakamakon.

“An jibge jami’ai a wuraren da ake zaton samun hargitsi, sun kuma yi shirin ko-ta-kwana don hana kowane irin tashin hankali ko zanga-zanga a jihar.

“Amma, za mu yi kira ga mutane da su kiyaye doka da oda, su kuma ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da jin tsoro ko firgici ba”, in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya bada rahoton cewa jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Sanata Ademola Adeleke sun ƙalubalanci nasarar da jam’iyyar APC da ɗan takararta, Gwamna Gboyega Oyetola suk samu a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan 2018 ta Jihar Osun.

A ranar 22 ga watan Maris ne kotun ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma sai wata Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin.

Daga nan sai aka mayar da shari’ar Kotun Ƙoli don yanke hukuncin ƙarshe, kotun ta shirya yanke hukuncin ranar 5 ga watan Yuli

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan