Home / Lafiya / Ko kun san dalilin da yasa Cutar Kwalara ke yi wa Kano barazana?

Ko kun san dalilin da yasa Cutar Kwalara ke yi wa Kano barazana?

Ƙananan ukumomi 27 daga cikin 44 na Jihar Kano sun samu ɓullar Cutar Kwalara a watan Yunin 2019, a cewar rahoton Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa, NCDC.

NCDC ta ce sakamakon binciketa ya nuna cewa Jihar Kano ce ke da mafiya yawan ƙananan hukumomi da ka iya kamuwa da ɓarkewar Cutar Kwalara a Najeriya.

An kafa Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa ne a shekarar 2011 don inganta shirin Najeriya na tunkarar annoba ta hanyar rigakafi, ganowa tare da daƙile cututtuka da ake iya ɗauka.

Manya-manyan ayyukan Cibiyar sun haɗa da gano, binciko, bada kariya tare da daƙile cututtuka da suka shafi al’ummar ƙasar nan gida da waje.

A cewar binciken na NCDC, jihohi16 suna da aƙalla ƙaramar hukuma ɗaya da ake gani a matsayin wajen da Cutar Kwalara ta yi katutu.

Kano ita ce ta farko a jerin jihohin, sai Kebbi, Sokoto, Borno, Zamfara da Kaduna.

Ƙananan ukumomi 27 na Jihar Kano ɗin sun haɗa da Fagge, Madobi, Dawakin Kudu, Kura, Ungoggo, Garun Malam, Kumbotso da Gezawa, duk a Kano ta Tsakiya.

Suran su ne Gwarzo, Ƙaraye, Shanono, Ɓagwai, Kabo, Rimin Gado, Tofa, Bichi, Dawakin Tofa a Kano ta Arewa.

Na ƙarshe su ne Wudil, Gaya, Tudun Wada, Rano, Bebeji, Bunkure, Kibiya, Doguwa, Rogo, da Ƙiru a Kano ta Kudu.

Me yasa Kano?
Wani masanin Likitancin Ƙasa, Dokta Uba Lawal ya shaida wa jaridar KANO TODAY cewa Jihar Kano ta zama jihar da Cutar Kwalara ke iya ɓarkewa ne saboda rashin tsafta da rashin kula da lafiya.

“Yin bahaya a fili, wanke hannaye ba da sabulu ba, da kuma yawan al’ummar Kano shi yake sa ƙwayar cutar Kwalara ta shiga cikin jikin ɗan Adam cikin sauƙi”, in ji shi.

Dokta Lawal ya ƙara da cewa za a iya samun waraka daga annobar Kwalara ta hanyar samar da tsaftataccen ruwan sha a birane da ƙauyuka.

Sauran matakan sun haɗa da ci gaba da wayar da kan jama’a wajen wanke hannaye da sabulu da kuma kula yadda al’umma ke yin bahaya.

About Hassan Hamza

Check Also

An ƙirƙiro Manhajar Bayar Da Bayanai A Kan Cutar Korona

Ƙungiyar Translators Without Boarders (TWB) ta ƙirƙiri wata manhaja da zata dinga taimakawa wajen bayar …

One comment

  1. Allah yaba mu lfy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *