Shugaba Muhammadu Buhari ya sake naɗa Injiniya Boss Mustapha a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF da Abba Kyari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, CoS.
Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ranar Juma’ar nan.
A cewar Mista Shehu, dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki ne tun ranar 29 ga Mayu, 2019.
Haka kuma, Shugaban ya naɗa wasu mataimakansa na musamman har 11 da suka haɗa da:
- Mohammed Sarki Abba –Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Gida da Taruka
- Ya’u Shehu Darazo – Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban (Ayyuka na Musamman)
- Dokta Suhayb Sanusi Rafindadi – Likitan Shugaban Ƙasa
- Ambasada Lawal A. Kazaure – Babban Jami’in Tsare-tsare na Fadar Shugaban Ƙasa
- Sabiu Yusuf – Mataimaki na Musamman (Ofishin Shugaban Ƙasa)
- Saley Yuguda – Mataimaki na Musamman (Kula da Gida)
- Ahmed Muhammed Mayo – Mataimaki na Musamman (Kuɗaɗe da Gudanarwa)
- Mohammed Hamisu Sani –Mataimaki na Musamman (Ayyuka na Musamman)
- Friday Bethel – Mataimaki na Musamman (General Duties)
- Sunday Aghaeze – Mataimaki na Musamman(Mai Ɗaukar Hoto na Fadar Gwamnati)
- Bayo Omoboriowo Mataimaki na Musamman (Mai Ɗaukar Hoton Shugaban Ƙasa)
Yawancin waɗanda suke a wannan jerin sunaye na baya-bayan nan dai sun yi aiki da Shugaban a wa’adin mulkinsa na farko.
Turawa Abokai