Kotun Ƙoli ta yanke hukunci game da rikicin zaɓen gwamnan Osun

118

A ranar Juma’ar nan ne Kotun Ƙoli ta tabbatar da zaɓen Gwamnan jihar Osun, kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola.

Alƙalai biyar daga cikin bakwai na Kotun sun goyi bayan zaɓen Mista Oyetola, yayinda guda biyu suka goyi bayan zaɓen ɗan takarar jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke.

Gungun alƙalai, waɗanda Alƙalin Alƙalan Najeriya, CJN, Ibrahim Muhammad ya jagoranta sun saurari ƙararrakin masu lamba SC/553/2019; SC/554/2019; SC/555/2019 da SC/556/2019.

Mista Adeleke ta hanyar tawagar lauyoyinsa waɗanda Dokta Onyechi Ikpeazu, SAN ya jagoranta, ya roƙi Kotun da ta yi watsi da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke ranar 9 ga watan Mayu, inda ta ce ba shi ya ci zaɓe ba, ya kuma roƙe ta da ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe wadda ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a Osun a watan Satumba, 2018.

Amma Mista Oyetola, jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC sun roƙi Kotun Ƙoli da ta yi watsi da ƙararrakin huɗu saboda rashin cancancta.

Mista Oyetola, ta hanyar tawagar lauyoyinsa, waɗanda Cif Wole Olanipekun, SAN ya jagoranta ya ce Kotun Ƙolin ta duba hujjojin da aka gabatar mata yadda ya dace kafin ta yanke hukuncin cewa shi ne sahihin ɗan takarar da ya lashe zaɓen.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan