Hukumar Hizba ta Kano na neman wasu ma’aurata da suka yi aure a Facebook a jihar ruwa a jallo

47

Hukumar Hizba ta Jihar Kano tana neman wasu ma’aurata da suka yi aure a Facebook a Jihar Kano ruwa a jallo, a cewar rahoton BBC Hausa.

Rahotanni sun ruwaito cewa wani Sunusi Abdullahi ne, ɗan shekara 29 daga Jihar Kano ya auri wata budurwa a Facebook, wadda ke amfani da Zainab Abu a Facebook ɗin, ‘yar Maidugurin Jihar Borno.

Abdullahi, wanda ana kuma kiran sa da General, yana amfani ne da Gen Sunus a Facebook, ya shaida wa BBC Hausa cewa da wasa ya ce yana so ya auri budurwar, bai san cewa maganar za ta zama babban al’amari ba.

“Abin ya fara ne daga hirar Facebook da aka saba yi da sauran abokai. Kawai sai ta ce in aure ta, abinda na amsa.

“Bayan ɗan wani lokaci, sai ta aiko min da saƙo, tana sanar da ni game da auren, ta ce ta samu wakili wanda zai tsaya mata don a yi auren. Saboda haka, ni ma sai abokina ya tsaya min a matsayin wakili.

“Daga nan sai muka yadda da sadakin N20,000, wanda na yi alƙawarin ba ta bayan an ɗaura aure. Mun bi dukkan ƙa’idojin aure, kuma aka ɗaura auren ta Intanet”, in ji shi.

A cewar Abdullahi, an yi ta ce-ce-ku-ce da tofa albarkacin baki bisa ingancin auren ko rashinsa.

“Wannan shi yasa na tuntuɓi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya tabbatar min da cewa auren bai ɗauru ba saboda an ɗaura shi ne ba tare da sani da amincewar iyayen amaryar ba”, ya ƙara da haka.

Abdullahi ya ce ya damu game da wannan batu har ba ya iya yin bacci.

Ya ƙara da cewa wadda zai aura a zahiri ta yi watsi da shi, yayinda shi ma wanda zai auri matar tasa ta Intanet ya yi watsi da ita sakamakon haka.

“Na san mun aikata babban kuskure. Ina neman gafara daga Alla, iyayena da al’umma gaba ɗaya. A halin yanzu, ba na tare da iyalina saboda iyayena sun fusata da abinda na yi”, ya bayyana haka.

Lokacin da BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sanusi Mohammed ya ce Hukumar ta umarci Hukumar Hizba da ta kama ma’auratan don yanke musu hukuncin da ya dace.

Ya ce hukuncin zai zama darasi ga sauran jama’a, yana mai cewa doka ta tanadi hukunci ga kowane irin laifi.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa batun ya raba kan malamai a jihar bisa sahihancin auren ko rashinsa, yayinda wasu ke bada kariya ga auren, wasu kuma sun yi watsi da shi, dukkan su suna masu jawo ayoyin Ƙur’ani da hadisan Annabi Muhammadu, tsira da amincin Alla su ƙara tabbata a gare shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan