Sabon Manajan Daraktan NNPC ya kama aiki

77

Sabon Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPC, na goma 19, Melee Kolo Kyari ya karɓi shugabancin kamfanin daga wanda ya rigaye shi, Maikanti Baru, wanda ya yi ritaya daga kamfanin ranar 7 ga watan Yuli, bayan cika shekaru 60.

Har lokacin naɗin sa, Mista Kyari shi ne Janar Manaja na Gungun Kamfanonin NNPC, Sashin Siyar da Ɗanyen Man Fetur. Shi ne kuma Wakilin Najeriya a Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur, OPEC tun shekarar 2018.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan