Wani shaida ya bayyana wa kotu yadda Atiku ya kada Buhari a zaɓen shugaban ƙasa a Katsina

187

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina, Salisu Maijigiri ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar jam’iyyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar ne ya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar ta Katsina da ratar ƙuri’a 33,000.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana a jihar ya nuna PDP ta samu ƙuri’a 308,056 yayinda jam’iyyar APC ta samu ƙuri’a 1,232,133.

To sai dai Mista Maijigiri, wanda ya bayyana haka a gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa dake Abuja ranar Talata, ya ce sakamakon da jam’iyyarsa ta tattara a jihar ya nuna cewa APC ta samu ƙuri’a 872,000 yayinda PDP ta samu 905,000.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar yana tsayawa ne a matsayin shaida na takwas a ƙarar da ake ci gaba da sauraro da aka shigar a Kotun mai alƙalai biyar, waɗanda Mai Shari’a Mohammed Garba ke jagoranta, inda ake ƙalubalantar nasarar Shugaba Buhari da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar.

“Mu (PDP) mu muka ci zaɓen ba APC ba.

“APC ta samu ƙuri’a 872,000, PDP kuma ta samu ƙuri’a 905,000.

“Waɗannan sakamakonmu ne na kan mu, da muka tattara a jiharmu, ba waɗanda “server” ta fitar ba”, in ji Mista Maijugiri.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan