Za a ɗaga likafar Muƙaddashin Alƙalin Alƙalai na Ƙasa

34

Majalisar Kula da Alƙalai ta Ƙasa, NJC, ta kammala wani taron tattaunawa na gaggawa ranar Larabar nan inda ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya naɗa Mai Shari’a I.T Muhammad a matsayin tabbataccen Alƙalin Alƙalan ne Ƙasa, wato CJN.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NJC, Soji Oye ya fitar ranar Laraba.

A cewar Mista Oye, taron tattaunawar, wanda da farko Mai Shari’a Umaru Abdullahi ya jagoranta, ya duba tare da amincewa da shawarar da Kwamitin Tantancewarta wanda ya tantance ‘yan takara biyu da Hukumar Kula da Alƙalai ta Ƙasa, FJSC ta gabatar.

Haka kuma, taron tattaunawar ya ba gwamnonin jihohin Sokoto, Legas, Anambra, Ebonyi, Naija, Taraba, Kano da Jigawa sunayen mutum takwas don naɗawa a matsayin Alƙalan Alƙalai da Granda Kadi a jihohin.

Sunayen su ne Mai Shari’a Muhammad S. Sifawa a matsayin Babban Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Sokoto; Mai Shari’a Kazeem Alogba, Babban Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Legas; Mai Shari’a Ijem Onwuamaegbu, Babban Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Anambra; Mai Shari’a Nwaigwe A. Anselm a matsayin Babban Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Ebonyi; Mai Shari’a Aliyu M. Mayaki a matsayin Babban Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Naija, da; Mai Shari’a Filibus B. Andetur, a matsayin Babban Alƙali, na Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Taraba.

Sauran su ne Onorabul Kadi Tijjani Yusuf Yakasai a matsayin Grand Kadi na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’ar Muslunci ta Kano; da Onorabul Isa Jibrin Gantsa a matsayin Grand Kadi na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’ar Muslunci ta Jihar Jigawa.

Mista Oye ya ce za a rantsar da sabbin Shugabannin Kotunan ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa da gwamnonin jihohinsu daban-daban, da kuma tabbatarwa daga Majalisar Dattijai da Majalisun Dokokin Jihohinsu.

Ya ce Majalisar ta yaba wa Shugaba Buhari saboda yadda ya ba Hukumomin Shari’a na Jihohi ‘yanci ta ɓangaren kuɗi, ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohin da su fara aiwatar da hakan cikin gaggawa.

Majalisar ta ƙara da ce wannan ba kawai ya yi dadai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki ba ne, amma shi ne ma matsayin Majalisar Shari’a.

Majalisar ta kuma karɓi sanarwar yin ritaya da Manyan Alƙalai na Babbar Kotun Tarayya ta jihohin Gombe, Edo, Naija, Ebonyi da Muƙaddashin Babban Alƙalin Jihar Kebbi suka bayar.

Ta kuma karɓi sanarwar ritaya da wasu jami’an shari’a su tara daga Babbar Kotun Tarayya da Manyan Kotunan jihohin Gombe, Delta, Edo, Imo, Benue da Katsina su ma suka bayar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan