Home / Siyasa / INEC ta fara shirye-shiryen zaɓen 2023- Farfesa Yakubu

INEC ta fara shirye-shiryen zaɓen 2023- Farfesa Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce Hukumar ta fara shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2023 duba da yadda ta fara yin bitar zaɓen 2019.

Mista Yakubu, wanda ya bayyana haka ranar Alhamis ɗin nan a Taron Tattaunawa na Yin Bitar Bayan Zaɓen 2019 da Kwamishinonin Zaɓen na Jihohi, RECs a Ikeja dake Jihar Legas, ya ce Hukumar ta lashi takobin inganta tsarin zaɓen ƙasar nan.

“Za ku iya tuna cewa mun yi alƙawarin za mu yi cikakkiyar bitar yadda muka gudanar da zaɓukan 2019 ta hanyar yi wa kai hisabi ciki da waje ta hanyar faɗaɗa tuntuɓa da masu ruwa da tsaki.

“A watanni 11 da rabi da suka gabata, mun yi tarukan tattaunawa har 11 a Abuja game da zaɓukan 2019. Tattaunawar yau da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi ita ce ta 12 kawo yanzu.

“A ƙarshen jerin waɗannan tarukan tattaunawa da tuntuɓa, mun gamsu cewa Hukumar za ta koyi wani muhimmin darasi game da gudanar da manyan zaɓuka- nasarori, matsaloli da mafita.

“Muna ganin waɗannan a matsayin wajibi saboda a matsayin Hukuma, muna ƙoƙarin ganin mun inganta tsarin zaɓen ƙasar nan.

“Mun gamsu cewa ana kammala zaɓen, ya kamata a fara shirye-shiryen yadda za a gudanar da zaɓe mai zuwa cikin gaggawa. Wannan a taƙaice shi ne abinda muke yi a waɗanda jerin tattaunawa”, in ji Mista Yakubu.

Ya ce Hukumar tana da ƙarfin guiwa da babban fatan cewa jami’anta na RECs, kamar sauran masu ruwa da tsaki za su yi abinda ake buƙata.

A ta bakinsa, taron tattaunawa na farko a jerin tarukan tattaunawar an yi shi ne a Abuja da jami’an RECs, jami’an Hukumar, dukkan turawan zaɓe daga ƙananan hukumomin ƙasar nan 774, shugabannin jam’iyyun siyasa, kafafen watsa labarai, ƙungiyoyin fararen hula, jami’an tsaro da sauransu.

Shugaban na INEC ya ƙara da cewa tun ranar 8 ga watan Yuli a Legas, Hukumar ta haɗu da kafafen watsa labarai, musamman editoci da jami’an tattara sakamakon zaɓe da masu sanarwa a ƙoƙarinta na ganin ta inganta tsarin zaɓen.

“Mun haɗu da Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya waɗanda suka yi aiki a matsayin jami’an tattara da sakamakon zaɓe a jihohi a Zaɓen Shugaban Ƙasa, kuma masu sanar da sakamakon zaɓen gwamnoni da kuma wasu manyan malaman manyan makarantu waɗanda suka yi aiki a matsayin jami’an sanar da sakamakon zaɓe a wasu mazaɓun ‘yan majalisu.

“Mun yi mitin da dukkan sakatarorinmu na mulki daga dukkan jihohin ƙasar nan da Babban Birnin Tarayya, FCT, Abuja da kuma taron ganawarmu na ƙarshe jiya, mun ji daga sassa 20 da cibiyoyi dake hedikwatar Hukumar a Abuja”, in ji shi.

A jawabinsa na maraba, Sam Olemekun, Kwamishinan Zaɓe na INEC, ya ce gudanar da zaɓukan 2019 ba zai kammala ba har har sai an yi bitar yadda aka yi zaɓen don samun mafita.

“Manyan zaɓukan 2019, a ra’ayina, an gudanar da su cikin nasara, kuma dole a yabi ƙoƙari da jajircewar Hukumar koda yake dai za a iya samun wasu abubuwa masu muhimmanci da ake buƙatar a duba a kuma yi bita don gudanar da zaɓe fiye da haka a nan gaba”, in ji Mista Olemekun.

A ta bakinsa, ‘yan siyasa ba su taimaka wajen gudanar da zaɓukan ba, ta yadda suka nuna tsananin son mulki da kuma ɗabi’ar a-mutu-ko-a-yi rai.

Ya ƙara da cewa yin garkuwa da jami’an tattara sakamakon zaɓe ko masu bayyana sakamakon zaɓen su faɗi sakamako bisa tilas zai ci gaba da kasancewa wani abin kunya kuma abin tir ga mutuncin zaɓukanmu.

A jawabinsa, Dokta Mustapha Lecky, Kwamishinan Ƙasa na INEC kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsare, Sa Ido da Dabaru, PMSC, ya ce yin bitar manufofi da tsare-tsaren zaɓukan da suka gabata zai zama wata shararriyar hanya wajen gudanar da zaɓukan gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi da manyan zaɓukan 2023.

“Wannan bitar hanya ce da za mu gane ƙarfinmu, rauninmu, damammakinmu da matsalolinmu.

“Haka kuma, za mu iya gano ƙalubale, tasgaro ko barazana da aka gano a a tsarin gudanar da zaɓen kafin, lokacin da bayan kammala zaɓukan 2019.

A saƙonta na fatan alheri, Monica Frassoni, Shugabar Cibiyar Tallafa wa Zaɓuka ta Ƙasashen Turai, ECES, ta ce Cibiyar tana ganin wata alfarma aka yi mata da ta kasance daga cikin waɗanda za a yi bitar da su, ta kuma taimaki INEC da tsarin zaɓe a Najeriya.

“2023 kamar da nisa, amma fa ba nisa. Yayin tattaunawar da muka yi a waɗannan kwanaki, mun ga cewa aikin da kuke da shi yana da wahala sosai, amma za a iya yin sa, kuma yana da ban sha’awa, kuma muna farin cikin tallafa muku a waɗannan aikace-aikace.

Shugabar Cibiyar ta ECES ta roƙi INEC da ta duba yiwuwar ƙara wasu tsare-tsare yayin da take shiryawa zaɓuka na gaba, tana mai cewa hakan zai inganta tsarin zaɓe.

“Wannan zai fara daga ɗaukar lokaci a saurara kuma a tattauna”, in ji ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya ruwaito cewa tarukan bitar sun samun halartar RECs, Kwamishinonin Ƙasa, Sakatarorin Mulki da sauransu.

About Hassan Hamza

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *