Buhari ya bayyana irin mutanen da zai naɗa a matsayin ministoci

36

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce daga yanzu ba zai ƙara naɗa mutanen da bai sani ba a matsayin ministoci.

A wata ganawa da shugabancin Majalisar Dokoki irinta ta farko, Shugaba Buhari ya ce mutanen dake da amana ne kaɗai za a sa a jerin sunayen sabbin ministoci.

A taron ganawar da aka yi a sabon Ɗakin Taro na Banquet Hall dake Fadar Shugaban Ƙasa ranar Alhamis da daddare, Shugaba Buhari ya ce an matsa masa lamba da ya kafa Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC.

Ya ce amma duk da wannan matsin lamba, waɗanda suke da tarihin gaskiya da amana ne kaɗai za a naɗa.

“Da yawan mutane a wannan liyafar cin abincin dare suna cewa suna son ganin jerin sunayen ministocin da ake son naɗawa don su tafi hutunsu cikin lumana.

“Ina sane da hakan sarai, ina fuskantar matsin lamba sosai game da naɗa ministocin. Amma Majalisar Ministoci da ta gabata wadda na jagoranta, mafi yawa daga cikinsu, ban san da yawansu ba. Dole na karɓi sunayen da shawarwari daga jam’iyya da sauran ɗaidaikun mutane.

“Na yi aiki da su tsawon shekara uku da rabi a ƙalla- mukan haɗu sau biyu ko duk bayan makonni biyu a wata. Saboda haka na san su.

“Amma wannan lokaci zan yi shiru, zan zaɓi mutanen da na son su”, in ji Shugaba Buhari.

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan majalisu da su haɗa kai da ɓangaren zartarwa wajen bar wa ƙasar nan abubuwa masu kyau, saboda wannan gwamnatin tasa ita ce ta ƙarshe.

Shugaban Ƙasar ya kuma shawarci ‘yan majalisun da su daina haɗa tsarin aikinsu na Majalisa da irin na ƙasashen da suka ci gaba a mulkin dimukoraɗiyya kamar Amurka da Birtaniya.

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, wanda ya yi wa manema labarai na Fadar Gwamnati jawabi jim kaɗan bayan ganawar sirrin, ya yi watsi da rahotannin kafafen watsa labarai da suka ce ya ce Shugaba Buhari zai miƙa sunayen ministocin ga Majalisar Dattijai a makon nan.

“Ya ce: “Wani sanata ya yi ƙorafi da yake buƙatar bayani na musamman.

“Ya ce ya kamata ɓangaren zartarwa ya turo mana da jerin sunayen ministoci, ni kuma a amsar da na bayar sai na ce ɓangaren zartarwar na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa an miƙa sunayen ‘yan Najeriya da za su taimaki wannan gwamnati, kuma za mu iya karbar sunayen a makon nan.

“Za mu iya’ tana nuna sharaɗi ne, zan kuma yi kira ga kowa da kowa da ya bada rahoto a haka”, in ji Mista Lawan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ovie Omo-Agege; Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamia da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase.

Akwai kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Kwamared Adams Oshimohole da sauran dogaran Shugaban Ƙasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan