Rukunin farko na maniyyatan bana na Kano sun isa Ƙasa Mai Tsarki

31

Rukunin farko na maniyyatan bana 534 sun isa Saudiyya ranar Juma’ar nan don gudanar da Aikin Haji na 2019.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa alhazan sun bar Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 10 na safe ta Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Max Airline a jirgi ƙirar Boeing 747.

Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba-Danbatta ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Juma’a a Kano.

A cewarsa, alhazan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 12 da suka haɗa da Doguwa, Bichi, Bebeji, Ɓagwai, Bunkure da Gabasawa.

Sauran su ne Garun Malam, Ƙaraye, Kumbotso, Shanono, Rano da Nasarawa.

Ya ce ana sa ran Kamfanin na Max Airline zai kai rukuni na biyu na maniyyatan Saudiyya ranar Asabar, 13 ga watan Yuli.

Mista Abba-Danbatta ya ce tuni Hukumar ta tanadi masauki mai kyau ga alhazan a Makka da Madina, ya kuma yi kira ga alhazan da su bi dokokin Saudiyya sau da ƙafa.

Shi ma Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gargaɗi alhazan da su guji aikata duk wani abu da ka iya zubar da mutuncin Jihar Kano da ƙasar nan a Ƙasa Mai Tsarki.

Mista Ganduje, wanda Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya yi gargaɗin ne yayinda yake yi wa maniyyatan jawabi a Sansanin Alhazai jim kaɗan kafin tashin su zuwa Ƙasa Mai Tsarki.

Ya shawarci alhazan da su kiyaye ɗaukar duk wani haramtaccin abu zuwa Saudiyya saboda hukumomin Saudiyya ba za su saurara wa duk wanda aka kama yana keta dokokin ƙasar ba.

Ya ce tuni Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kotun tafi-da-gitanka don hukunta alhazai masu kunnen ƙashi a Ƙasa Mai Tsarkin a matsayin wani ɓangare na tabbatar da ɗa’a tsakanin alhazan, ya bayyana fatan cewa za su nuna halin ƙwarai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan