Yadda wasu mazauna gidan yari suka kammala karatu a Jami’ar NOUN

157

Cibiyar Karatu ta Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya, NOUN, dake Gidan Yarin Enugu ta yi kira da a samar da matsugunai na musamman ga mazauna gidan yarin dake karatu a Cibiyar.

Kevin Iloafonsi, Shugaban Cibiyar ya bayyana haka ranar Alhamis ɗin nan a yayin miƙa Takardun Shaidar Kammala Karatu ga wasu mazauna gidan yarin huɗu waɗanda suka kammala karatu a Jami’ar ta NOUN.

Mista Iloafonsi ya roƙi da a gina ɗakin kwanan ɗalibai a Cibiyar don amfanin irin waɗannan mazauna gidan yarin.

Ya ce kiran ya zama wajibi saboda buƙatar da ake da ita na samar da kyakkyawan yanayi don inganta karatun mazauna gidan yarin.

“Muna neman amincewa a samu ɗakin kwanan ɗalibai na musamman, ba ɗakin ajiye masu laifi ba ga dukkan ɗaliban NOUN dake nan don ba su dama su haɗu da masu ƙwaƙwalwa irin tasu su kuma kafa gungun karatu”, in ji shi.

Mista Iloafonsi ya ce a shekara takwas da kafa Cibiyar Karatun ta samu manyan nasarori da kuma matsaloli.

A ta bakinsa, yawan ɗaliban ya ƙaru daga ɗalibai mazauna gidan yari 12 a shekarar karatu ta 2011/2012 zuwa ɗalibai 191 a shekarar karatun da ake ciki.

Ya ce Cibiyar Karatun ta fuskanci matsalar kayayyakin more rayuwa saboda yadda ɗakin ɗaukar karatunsu ya lalace.

Shugaban Cibiyar ya ce bugu da ƙari kuma, ɗakin ɗaukar karatun tsohon ɗakin ajiye masu laifi ne aka mayar ɗakin ɗaukar karatu.

Mista Iloafonsi ya ce suna kuma buƙatar malamai saboda sun dogara ne da matasa masu yi wa ƙasa hidima a matsayin malamai.

A saƙonsa na fatan alheri, Babban Daraktan Ƙungiyar Kula da Buƙatun Mazauna Gidan Yari ta Carmelite, CAPIO, Rev. Fr. Ambrose Ekeroku, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar ta Enugu da ta dawo da makarantar sakandire a gidan yarin.

Ya ce wajibi ne a samar da ilimi na kowane mataki ga mazauna gidan yarin da yawansu ya kai 2000.

Malamin na addinin Kirista ya ce a baya gidan yarin yana da makarantar sakandire, yana mai ƙarawa da cewa ba a bada wani dalili da yasa aka kulle makarantar ba.

Tun da farko, Ndubuisi Ogbodo, Kwanturola na Gidajen Yari, na Rundunar Jihar Enugu, ya ce NOUN ta taka muhimmiyar rawa wajen gyara halayen mazauna gidan yari.

Mista Ogbodo ya ce Cibiyar ta samar da ɗalibai da yawa, yana mai ƙarawa da cewa a kwanan nan ne Kwamitin Gyara Gidajen Yari da Rage Cunkoso da Shugaban Ƙasa ya kafa ya saki wasun su da suka samu damar iya komawa cikin al’umma.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Uba Adamu, lokacin da yake bada Takardun Shaidar Kammala Karatun ga ɗaliban, ya ce Jami’ar nada buɗaɗɗiyar manufa.

Mista Adamu, wanda Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Justus Shojefun ya wakilta, ya yi kira ga ɗaliban da suka cancanta, amma har yanzu ba su shiga Jami’ar ba da su shiga.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa daga cikin ɗaliban huɗu da suka kammala karatu, an ba uku shaidar Kammala Karatun Digiri na Ɗaya, yayinda ɗaya ya samu Shaidar Kammala Karatun Digiri na Biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan