Majalisar Dattijai ta amince da sunan wani wanda ba shi da sahihan takardun shaidar karatu

154

A ranar Alhamis ɗin nan ne Majalisar Dattijai ta 9 ta tabbatar da Aliyu Saidu Abubakar a matsayin Ƙaramin Kwamishinan Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Ƙasa, wato NCC.

Majalisar Dattijai ta 8 wadda Dokta Abubakar Bukola Saraki ya jagoranta ta ƙi amincewa da shi sakamakon kasa kawo sahihan takardun shaidar kammala karatu.

A watan Nuwamba, 2016 ne aka yi watsi da sunan Mista Abubakar.

Tabbatarwar da Majalisar Dattijan ta yi ya biyo bayan amincewa da rahoton Sanata Teslim Folarin, wanda ya tantance shi.

Sauran da suka samu tantancewa tare da Mista Abubakar daga Majalisar sun haɗa da Injiniya Uba Masaka a matsayin Babban Kwamishina, Farfesa Millionaire Abowei da Abdulazeez Mohammad Salman.

A baya dai, Shugaban Kwamitin NCC na Majalisar Dattijai ta 8, Barth Nnaji ya ce Mista Abubakar ba shi da ƙwarewa ta fuskar aiki da karatu da ake buƙata a Sashi na 7 (1) (a-h) na Dokar da ta kafa Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa, NCC ta 2003, wadda ta sa ƙa’idoji bisa cancantar mambobin Hukumar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan