Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta yi sabbin naɗe-naɗe

179

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA, ta sanar da wani babban sauyi ta ɓangaren gudanarwa inda ta naɗa Janar Manajoji, GMs da Mataimaka Janar Manajoji, AGMs don inganta aikin Hukumar.

Janar Manaja na Sashin Dabarun Sadarwa na Hukumar, Adams Jatto ya sanar da haka a wata sanarwa da ya bayar ranar Juma’a a Legas.

A ta bakinsa, naɗin ya zo bayan wasu naɗe-naɗe da canjin wuraren aiki da aka yi wa wasu jami’an tashoshin jiragen ruwa da manyan ma’aikata.

“Da wannan ci gaba, a yanzu A’isha Ali Ibrahim ta zama GM- Marine and Operations; Captain Jerome Angyunwe- GM Health, Safety and Environment; Malam Isah Suwaid Ali- GM Superannuation; Musa Yaro- GM Procurement da Mohammad Kabiru Kolo- Audit.

“Sauran sun haɗa da Olumide Omotosho – GM Security; Mista Sylvanus Ezugwu – GM Finance; Misis Nana Yakubu – GM Public Private Partnership; Misis Christiana Akpa – GM Medicals, da Mr Innocent Gamboro – GM Corporate and Strategic Planning.

“A ɓangaren Mataimaka Janar Manajoji, AGMs, Ayodele Duruwaiye ya zama AGM Operation; Misis Zainab Kwande- AGM Servicom; Mista Hassan Danjuma- AGM Corporate and Strategic Communication; Mista Talum Amos- AGM Hydrographic; Mista Jamil Khalil- AGM Security; Injiniya Suleiman Anas- AGM Corporate and Strategic Planning; da Mista Shehu Mohammed- AGM Public and Private Partnership.
“Sauran da suke a ɓangaren Mataimaka Janar Manajoji su ne Chuma Ezeneinyinya – AGM Occupational Health; Dokta Chinwe Nwokolo – AGM Medical Services; Capt. Sylvester Owobu – AGM Marine; Izegboya Ethel – AGM Board; Felix Onyile – AGM Human Resources; Mr Sani Isu – AGM Land and Estate”, in ji sanarwar.

A ta bakin Mista Jatto, sauran waɗanda aka naɗa a muƙaman Mataimaka Janar Manajoji su haɗa da; Tokunbo Akingbuwa – AGM Budget; Olusola Dairo – AGM Performance Management; Akinlabi Illesanmi – AGM Civil; da Misis Lucy Gukas – AGM Tariff and Billing.

Ya ce naɗe-naɗen sun yi daidai da manufar tsarin karɓa-karɓa na Manajan Daraktan NPA, Hadiza Bala Usman domin cike guraben shugabanci da ake da su sakamakon ritaya da wasu manyan jami’an Hukumar suka yi.

Naɗa sabbin ma’aikatan zai inganta tsarin shugabanci na Hukumar, ya kuma samar da sabbin dabarun aiki da za su ciyar da NPA ɗin gaba a ƙoƙarinta na zama jagora a ɓangaren sufurin jiragen ruwa a Afirka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan