Wata mata a Kano ta faɗa rijiya ta mutu yayinda take faɗa da kishiyarta

197

Wata mata a ƙauyen Tarunge dake ƙaramar hukumar Rogo a Jihar Kano ta mutu yayinda take faɗa da kishiyarta.

Wani rahoto da aka bayar a shirin In Da Ranka na Freedom Radio ya ce duka kishiyoyin suna cikin faɗa ne lokacin da suka faɗa rijiyar.

Wani maƙobci, Isah Yahaya ya faɗa wa manema labarai cewa sun ceto ɗaya daga cikin matan a raye, suka kuma fito da gawar ɗayar.

Mista Yahaya ya ce tuni an miƙa matar da ta tsira da wadda ta mutun ga ‘yan sanda don bincike.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan