An fara jigilar maniyyatan bana na Gombe

221

Jihar Gombe ta kai rukunin farko na maniyyatan jihar da adadinsu ya kai 560 zuwa Saudiyya.

Maniyyatan sun tashi ne ta Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Lawanti dake Gombe.

Alhaji Sa’adu Hassan, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar ya faɗa wa manema labarai cewa maniyyatan za su sauka ne a Madina, inda tuni an kammala shirye-shiryen yadda jami’an Hukumar Aikin Haji ta Ƙasa, NAHCON za ta karɓe su.

A ta bakinsa, ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli ne za a kai rukuni na biyu na maniyyatan zuwa Saudiyyar.

Ya yi kira ga sauran maniyyatan dake zaman jira da su ƙara haƙuri, su kuma fito duk lokacin da aka buƙace su.

Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar, Amirul Hajji kuma Sarkin Gombe ya shawarci maniyyatan da su bi dokoki da ƙa’idoji yayin zamansu a Ƙasa Mai Tsarki.

Ya yi kira a gare su da su yi amfani da abinda suka koya yayin koyar da su aikin Hajin a nan gida.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya ruwaito cewa Jihar Gombe nada jimillar maniyyata 1,460 waɗanda za su sauke farali a aikin Hajin bana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan