Home / Ilimi / NiMet ta fitar da rahoton yanayin da za a iya samu yau Lahadi

NiMet ta fitar da rahoton yanayin da za a iya samu yau Lahadi

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa, NiMet ta yi hasashen samun yanayin gajimare a safiyar Lahadin nan.

Rahoton yanayin da NiMet ta fitar ranar Asabar a Abuja ya yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a faɗin ƙasar nan da rana da yamma a ranar ta Lahadi.

A cewar Hukumar, ana sa ran samun tsawa a jihohin Katsina, Kano, Jigawa da Maiduguri dake Arewacin Najeriya a safiyar Lahadi, da kuma yanayin gajimare sama-sama a sauran yankunan.

Ta yi hasashen samun tsawa a Gusau, Sokoto da Kebbi a ranar ta Lahadi, inda yanayin zafi da sanyi zai kai digiri 29 zuwa 32 a ma’aunin Celcius da kuma digiri 21 zuwa 25 a ma’aunin na Celcius.

Rahoton ya ce ana hasashen samun ruwan sama a safiyar Lahadin a Ilori da Bidda dake jihohin Tsakiyar Najeriya.

Ta kuma yi hasashen samun tsawa a dukkan faɗin yankin da rana, inda yanayin zafi da sanyi zai kai digiri 27 zuwa 31, da kuma digiri 16 zuwa 24 a ma’aunin na Celcius.

Hukumar ta kuma yi hasashen samun yanayin gajimare a Jihohin Kudancin Najeriya da safe, da yiwuwar samun ruwan sama a layukan Osogbo da Shaki.

“A dai ranar Lahadin, ana sa ran samun ruwan sama a wannan yankin.

Yanayin zafi da sanyi na rana da dare zai kai digiri 28 zuwa 31 a ma’aunin Celcius, da kuma digiri 21 zuwa 23 a ma’aunin na Celcius”, NiMet ta yi hasashen haka.

About Hassan Hamza

Check Also

Bayan Kwashe shekaru 27 a ƙarshe Bill Gates ya saki matarsa Melinda

Bill Gates, wanda da shi aka kirkiri kamfanin Microsoft, da matarsa, sun amince za su …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *