Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta karrama wani jami’inta sakamako nuna halin ɗa’a da ya yi

169

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta shirya tsaf don karrama ɗaya daga cikin jami’anta, Aircraftman, ACM Bashir Umar, wanda ya tsinci Euro 37,000, kuma ya mayar da su ga mamallakinsu, Alhaji Ahmad.

Rundunar Sojin Saman ta bayyana haka ne a wata sanarwa da Daraktan Huɗda da Jama’a da Yaɗa Labarai na Rundunar, Ibekunle Daramola ya sanya wa hannu, aka wallafa a shafin Facebook na Rundunar ranar Lahadi.

Al’amarin dai ya faru ne a Kasuwar Sansanin Alhazai ta Kano ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019, lokacin da ACF Umar, wanda memba ne na NAF Mobile Air Defence Team, MADT, da aka turo domin aikin tsaro a filin jirgin sama, yayinda yake kan rangadi da shi da wasu abokan aikinsa ya tsinci kuɗin a wata jaka, bai yi wata-wata ba sai ya miƙa kuɗin ga mai su.

Sakamakon haka, Baban Hafsan Sojin Ruwa, CAS, Air Marshal Sadique Abubakar, ya umarci Shugaban Sashin Gudanarwa a Hedikwatar Rundunar, Air Marshal Kingsley Lar da ya kawo tsare-tsaren yadda za a karrama wannan jami’in sojin sama don a ƙarfafa wa sauran jami’an Rundunar su ci gaba da kwaikwayon halayen mutunci, hazaƙa da aiki da aka san Rundunar da su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan