Wani kwamandan Sojin Najeriya ya ja kunnen ‘yan Boko Haram su miƙa wuya

138

Majo Janar Bulama Biu, Shugaban 7 Division ta Rundunar Sojin Najeriya ya sabunta gargaɗinsa ga ‘yan Boko Haram cewa su miƙa makamansu.

Mista Biu ya yi kiran ne a wani biki da aka shirya don girmama shi ranar Asabar a Gidan Karɓar Baƙi na Rundunar dake Sansanin Soji na Maimalari, a Maiduguri.

A makon da ya gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ciyar da Mista Biu da sauran jami’ai gaba saboda irin gudummawar da suke bayarwa wajen yaƙi da ta’addanci.

Kimanin mutane miliyan biyu ne suka rasa gidajensu, wasu dubbai kuma sun rasa rayukansu tunda aka fara rikicin Boko Haram a 2009.

Mista Biu ya ce rikicin na Boko Haram da ya kai shekaru 10 yanzu ya yi mummunan tasiri ga rayuka da dukiyoyi, saboda haka sai ya yi kira ga tsagerun na Boko Haram da su ci gajiyar damammakin Shirin Afuwa da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi ƙarƙashin “Operation Safe Corridor”.

“Har yanzu kuna da dama ku miƙa malamanku; yanzu ne lokacin miƙa wuya, don a ba ku damar komawa cikin al’umma”, in ji shi.

Mista Biu ya yi gargaɗin cewa idan ‘yan Boko Haram suka ci gaba da kai hare-hare, to fa sojoji a shirye suke su murƙushe su.

Yayinda yake jinjina wa dakarun sojin ƙasar nan bisa irin jajircewarsu da sadaukarwa, Mista Biu ya jaddada shirin dakarun sojin na kawo ƙarshen rikicin Boko Haram, su kuma dawo da zaman lafiya a yankin da yaƙi ya galabaita.

Ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa yadda ya ɗaga likafarsa zuwa Majo Janar, ya kuma gode wa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, CoAS, Laftanar Janar Yusuf Burutai bisa yadda ya ba shi Kyautar Yabo.

Kwamandan ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Borno, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa irin gudunmawar da suke bayarwa a yaƙi da ta’addanci.

Majo Janar Benson Akinroluyo, Theatre Commander na Operation Lafiya Dole, ya yaba wa Mista Biu bisa jajircewarsa, shugabanci mai nagarta da nuna ƙwarewa wajen yaƙi da ta’addanci.

Mista Akinroluyo ya siffanta Mista Biu a matsayin “mutumin dake ba dakrunsa umarni daga sahun gaba, ba na baya ba”.

Shi ma Gwamna Umara Zulum ya yabi Rundunar Sojin bisa irin nasarar da ta samu a yaƙi da ta’addanci.

Wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Alhaji Umar Kadafur, Gwamnan ya yi alƙawarin tallafa wa aikin Rundunar Sojin na dawo da zaman lafiya a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan