Ko kun san yadda Kotu ta saurari ƙarar Abba Kabir Yusuf a yau?

122

A ranar Litinin ɗin nan ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Zaɓen Gwamna na 23 ga watan Maris a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da hujjoji har 241 a Gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar.

Mista Yusuf da jam’iyyarsa ta PDP suna ƙalubalantar nasarar da Dokta Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ya samu a Zaɓen Gwamnan.

Waɗanda ake ƙara a ƙarar su ne Ganduje, APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.

Lauyan masu ƙara, Adeboyega Owomolo mai lambar SAN, wanda ya gabatar da hujjojin a gaban Kotun, ya ce tim ɗinsa yana fatan kawo ƙarin hujjoji don su tabbatar da abinda suke ƙara.

Mista Owomolo ya faɗa wa Kotun cewa daga cikin hujjojin nasu akwai sahihan sakamakon zaɓe da aka samo daga mazaɓu dake ƙunshe a Form EC8As da Form EC8Bs daga ƙananan hukumomin Albasu, Bebeji, Bichi, Ɗanbatta, Garun Malam, Gwarzo, Ƙaraye, Kura, Madobi, Nasarawa, Rano, Rogo, Sumaila, Tudun Wada da Warawa da sauransu.

Lauyoyin waɗanda ake ƙara, Offiong Offiong da Ahmad Raji dukkaninsu masu lambar SAN ya soki gabatar hujjojin.

Mista Offiong ya faɗa wa Kotun cewa ya masu ƙara sun kawo wa Kotun jakunkuna ne, ba wai sahihan takardun sakamakon zaɓe ba.

“Masu ƙarar ba su kawo mana takardun mu gani ba, jakunkuna kawai suka kawo, ni abinda ya dame ni shi ne abinda ke ciki”, in ji shi.

Amma, Shugabar Kotun, Mai Shari’a Halima Shamaki, ta yi watsi da sukar hujjojin, ta kuma karɓi takardun a matsayin hujja, sannan ta ɗaga zaman Kotun zuwa 23 ga watan Yuli don ci gaba da sauraron ƙarar.

A ƙalla shaidu 785 ake sa ran za su zo gaban Kotun don bada shaida ga APC da PDP game da yadda aka gudanar da Zaɓen Gwamna na watan Maris na 2019

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan