Sahad Stores ya kori ma’aikatansa sakamakon ɓatan wasu maƙudan kuɗaɗe

126

Shahararren kantin siyar da kayayyakin nan, Sahad Stores, ya kori wani manaja da sauran ma’aikata 74 bisa ɓatan wasu maƙudan kuɗaɗe har Naira Miliyan 250, a cewar jaridar DAILY NIGERIAN.

Wakilin jaridar ya gano cewa an kori dukkan ma’aikatan reshen kantin dake Zoo Road da Mandawari a Kano.

An ɗauki wannan mataki ne ranar 4 ga watan Yuli, biyo bayan binciken kantin da na kuɗi da aka saba yi duk shekara, wanda ya nuna wasu kuɗaɗe sun ɓata.

Shugaban Rukunin Kantunan na Sahad Stores, Ibrahim Mijinyawa ya tabbatar wa da DAILY NIGERIAN korar ma’aikatan, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan da ya gano cewa wasu kuɗaɗe sun ɓatan bayan gudanar da binciken kuɗi da ake yi duk shekara.

“Maganar da nake da kai yanzu, na maye gurbin su gaba ɗaya, har da manajan. Abu ne mara daɗi, saboda dukkanninmu sai mu karɓi ƙaddara.

“Na ji cewa sabon manajan ya ƙara ɗaukar wasu daga cikinsu aiki. Wannan matakinsa ne. Ba mamaki ya amince da su. Idan suna so su yi iƙirarin diyyarsu, sai su ci gaba. Ba na son matsala, kuma ba na so in yi faɗa da ma’aikatana”, in ji shi.

Amma ɗaya daga cikin waɗanda korar ta shafa, Fatihu Hafizu, ya ce Mista Mijinyawa ya kore su ne ba tare da aika musu da takardar neman bahasi ko faɗa musu laifinsu ba.

Ya ce daga bisani sai aka faɗa musu cewa Naira Miliyan 250 ta ɓata bayan an yi binciken kuɗi, wani yanayi da ya fusata Mista Mijinyawa ya kore su.

A cewar Hafizu, tunda aka kafa Sahad Stores kimanin shekaru 30 da suka gabata, an saba yin binciken kaya da na kuɗin duk shekara, amma ba a taɓa samun asara ba.

Ya kuma ce duk shekara ma’aikatan suna karɓar garaɓasa don zaburarwa, banda wannan shekarar da aka saka musu da takardun kora.

“Amma wannan shekarar, mun ga wani abu daban. Ana gama binciken kuɗin, sai Shugaban ya kira mu zuwa taron tattaunawa, sannan ya sanar da korar mu.

“Sai aka bar mu muna mamakin me yasa ya ɗauki wannan tsattsauran mataki bayan wasu daga cikinmu sun shafe shekara 20, wasu 15, wasu ma 25 a kamfanin nan ba tare da samun su da matsalar kuɗi ba.

“Ba mu san abinda ya faru ba. Bayan nan ne sai muka ji cewa Naira Miliyan 250 ta ɓata bayan an kammala binciken kuɗi. Na rantse da Allah haka ba ta faru ba”, in ji shi.

Daga nan sai Hafizu ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abudullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da su sa baki a al’amarin.

Ya lura da cewa da yawansu suna da iyalai a ƙarƙashin su, yana mai cewa korar za ta shafi iyalansu.

Wannan tsohon mai tsaron kanti ya yi kira ga Mista Mijinyawa da ya biya su kuɗaɗen sallama daga aiki don ba su damar fara ƙananan sana’o’i don su kula da iyalansu.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa an kulla reshen kantinan biyu na ɗan wani lokaci, amma aka sake buɗe su bayan an canza ma’aikatan gudanarwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan