Buhari ya miƙa ƙunshin sunayen ministoci ga Majalisar Dattijai

153

Shugaba Muhammadu Buhari ya miƙa sunayen mutum 43 ga Majalisar Dattijai don tabbatar da su a matsayin ministoci.

A ranar Talatar nan ne Majalisar Dattijai ta bayyana sunayen.

Waɗanda suke a sama a jerin sunayen sun haɗa da Gbemisola Saraki, ‘yar uwar tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Dokta Abubakar Bukola Saraki; tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola; Festus Keyamo; da tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio.

Haka kuma akwai George Akume, Niyi Adebayo, Olutayo Alasoadura, Adeleke Mamora da kuma waɗanda za su ƙara dawowa a matsayin ministoci, Rotimi Amaechi, Raji Fashola, Chris Ngige da Lai Mohammed.

Sauran da sunayensu suka fito a jerin sunayen su ne Time Sylva, Baba Mustapha, Abba Goddy, Dokta Ogbonnaya Onu, Godfrey Onyeama, Suleiman Adamu, Emeka Nwaojoba, Zainab Ahmed, Mohammed Mahamud, Had Sirika, Abubakar Malami, Olamilekan Adegbite, Zubair Dada da Sunday Dare.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan