Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Mohammed Tanko a matsayin tabbataccen Alƙalin Alƙalan Najeriya, CJN.
Mista Mohammed, wanda aka rantsar a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja ranar Laraba ya zama Alƙalin Alƙalai na 18.
A makon da ya gabata ne Majalisar Dattijai ta tantance tare da amincewa da Mista Mohammed, wanda ya gaji tsohon Alƙalin Alƙalai, Walter Onnoghen.
Tun a watan Janairun bana ne ya zama Muƙaddashin Alƙalin Alƙalai.
Ya samu muƙamin CJN ne bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen bisa zarginsa da ba dai-dai ba a wajen bayyana kadarorinsa.
Turawa Abokai