Ganduje ya biya wa ɗaliban Kano dake karatu a Sudan kuɗin makaranta

246

Gwamnatin Jihar Kano ta biya fiye da Naira Biliyan 2 na bashin kuɗin makaranta ga ɗalibanta dake karatu a Jami’ar El-Razi dake Sudan.

Gwamnatin tsohon Gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ta bar wannan bashi.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Hukumar Amintattau ta Jami’ar El-Razi, Farfesa Ibrahim Ghandour ranar Talata a Kano.

“Gwamnatina ta gaji ɗalibai daga gwamnatin da ta gabata da kuɗaɗe da yawa da ba a biya ba.

“Ta hanyar alaƙa mai kyau tsakanin Jami’ar da Jihar Kano, mun iya biyan wannan jimillar kuɗaɗe don ɗalibanmu su kammala karatunsu.

Mista Ganduje, wanda Mataimakinsa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya kusan kaso 80 cikin ɗari na dukkan kuɗaɗen makaranta na ɗalibanta dake Indiya, Masar da Cyprus, waɗanda su ma gadar su ta yi daga gwamnatin da ta gabata.

Gwamnan ya ƙara da cewa a kwanan nan ma gwamnatin ta biya fiye da Naira Miliyan 300 ga Jami’ar Cyprus don ba ɗalibai da Jihar Kano ta ɗauki nauyinsu su kammala karatunsu.

Ya ja hankalin ɗaiɗaikun mutane dake siyasantar da batun ilimi a jihar, yana mai cewa irin wannan halayya ba za ta amfani Jihar Kano ba ko ƙasar nan ta kowace hanya.

“Abinda ke da muhimmanci shi ne ba wai siyasantar da wani ɓangare na ilimi ba, duk wanda zai yi suka, ya kamata ya yi suka mai ma’ana saboda ba wanda yake cikakke. Yanzu da muka yi haƙuri, ga shi mun biya kuɗin”, in ji shi.

Yayinda yake bayyana jin daɗi game da kyakkyawar alaƙa tsakanin Sudan da Najeriya, Mista Ganduje ya tabbatar wa da Jami’ar El-Razi cewa za a ci gaba da samun ɗaliban Jihar Kano masu ƙwazo a wajen karatu da hali na gari.

Game da Digirin Girmamawa da Jami’ar ta ba shi, Gwamnan ya ce wannan girmamawa ce da aka yi wa dukkan al’ummar Jihar Kano.

Tun da farko, Professor Ghandour ya ce sun zo Kano ne don su bayyana jin daɗinsu bisa kyakkyawar alaƙa da ake da ita tsakanin Jami’ar da Gwamnatin Kano tsawon shekaru.

“Maƙasudin zuwan mu nan shi ne mu gabatar wa Mai Girma Digirin Girmamawa.

“A yanzu, shekarar Jami’ar El-Razi 23, ta yaye ɗalibai a Ilimin Likitanci da na Haɗa Magunguna, amma wannan shi ne Digirin Girmamawa mafi daraja da aka taɓa ba wani mutum a wajen ƙasar nan”, a kalaman Farfesa Ghandour.

Ya ce ranar 26 ga watan Agusta, 2019 ne za a bada wannan Digirin Girmamawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan