Gwamna Bagudu ya sa ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kebbi

141

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, KESIEC ta sa ranar 26 ga watan Agusta, 2019 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Kwamishina mai kula da Kafafen Watsa Labarai da Huɗda da Jama’a na KESIEC, Alhaji Kabiru Muhammad ya sanar da haka ga manema labarai ranar Laraba a Birnin Kebbi.

Ya ce an amince da ranar ne a wani taron tattaunawa da aka yi kwanan nan da jami’an gudanarwa Na Hukumar.

Mista Muhammad ya ce za a iya samun fama-faman takara da sauran sauran fama-famai dake da dangantaka da zaɓen a Sakatariyar Hukumar dake Birnin Kebbi.

“An yi wannan ne don a ba jam’iyyun siyasa, masu ruwa da tsaki da al’umma gaba ɗaya su lura su kuma fara dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don fuskantar zaɓen mai zuwa”, in ji shi.

Kwamishinan ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da al’umma gaba ɗaya da su bada haɗin kai don gudanar da zaɓe karɓaɓbe.

Zaɓe na ƙarshe da Hukumar ta gudanar a ƙananan hukumomi 21 na jihar shi ne na ranar 15 ga watan Yuli, 2017.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan