Home / Siyasa / Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamna a Kogi ya bar jam’iyyar

Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamna a Kogi ya bar jam’iyyar

A ranar Larabar nan ne Dokta Idris Omede, mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takara a zaɓen gwamnan da za a gabatar ranar 16 ga watan Nuwamba ya sanar da cewa bar jam’iyyar.

Mista Omede, tsohon Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa, NMA, ya faɗa ranar Laraba a wani taron manema labarai a Abuja cewa ana ci gaba da tattaunawa don ganin an samu jam’iyyar da ya kamata ya gwada sa’arsa.

Ya ce ya bar jam’iyyar ne saboda yadda ake neman lalata tsarin yadda za a gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Mista Omede ya ce a fili yake cewa jam’iyyar PDP a jihar ba ta koyi darasi da ya kawo ta halin da take ciki a yanzu ba.

A cewarsa, a fili yake cewa wasu abubuwa suna kan kuskure, kuma jam’iyyar ba ta yi wani shiri na gyara su ba, tana yi musu ruƙon sakainar kashi.

Mai neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar ya zagi wakilan jam’iyyar da yunƙurin azurtata kansu daga dukkan masu neman jam’iyyar ta tsayar da su takara kafin da kuma yayin gudanar da zaɓen fitar da gwani mai zuwa.

About Hassan Hamza

Check Also

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *