Akwai ‘yan Shi’a a cikin sunayen ministoci, kar ku tantance su- Ƙungiyar Izala ta faɗa wa Majalisar Dattijai

42

Ƙungiyar Izalatul Bid’a Wa Iƙamatus Sunnah, JIBWIS da aka fi sani da Ƙungiyar Izala ta ankarar da Majalisar Dattijai cewa akwai wasu mambobin Islamic Movement of Nigeria, IMN, wato ‘yan Shi’a a cikin jerin sunayen ministocin Shugaba Muhammadu Buhari, tana mai kira ga ‘yan majalisun da su yi watsi da sunayen.

JIBWIS ɗin, ta bakin Shugaban Majalisarta ta Malamai ta Ƙasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ta bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa dake Jos, a wani mayar da martani ga ƙarin kashe-kashe da ke ƙaruwa tsakanin ‘yan Shi’ar da ‘yan sanda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a artabun da aka yi kwanan nan tsakanin ‘yan Shi’ar da ‘yan sanda, an bada rahoton kashe mutane 13, da ya haɗa da wani babban jami’in ɗan sanda, da wani mai ɗaukar rahoto na Gidan Talabijin na Channels, Owolabi.

Koda yake dai jami’in na JIBWIS bai ambaci sunaye ba, ya ce: “Mun gano cewa a cikin sunayen sabbin ministocin, akwai ‘yan Shi’a, waɗannan sunaye bai kamata a tabbatar da su ba.

Malamin addinin Musuluncin ya yi kira ga Majalisar Dokokin ta Ƙasa da ta yi watsi da sunan duk wani minista da yake da alaƙa da Shi’a.

Daga nan sai Sheikh Jingir ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya ɗauki dukkan matakan da suka wajaba a kan ‘yan Shi’ar, yana mai cewa aikace-aikacensu sun nuna cewa ba masu kishin Najeriya ba ne.

Ya ce: “Iran ce take zuga su, kuma ina so su san cewa ‘yan Iran ba za su riƙa kai wa ƙasarsu hari ko kuma su yi yunƙurin kashe shugabansu kamar yadda ‘yan Shi’a a Najeriya ke yi.

“Abin kaico ne a ce wasu ‘yan ƙasa suna ɗaukar makamai a kan ‘yan sandansu, suna so su kai wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa hari, suna kuma cewa za su kashe ‘ya’yan Shugaban Ƙasa ko ma Shugaban Ƙasar da kansa.

“Ba ma so Shugaba Buhari ya yi wa wannan batu sako-sako; ya kamata ya ɗauki matakan da suka wajaba don tabbatar da cewa jami’an tsaro da dukkan waɗanda suka dace sun kawo ƙarshen batun ‘yan Shi’a da gaggawa”.

A cewarsa, JIBWIS, a matsayinta na ƙungiyar Musulunci, ba za ta naɗe hannayenta ta ƙyale abubuwa su taɓarɓare ba tare da ta bada shawarar da ta dace ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan