Muna goyon bayan shirin TRCN na hana malaman da ba su da ƙwarewa koyarwa- NUT

160

Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa, NUT, ta ce za ta haɗa kai da Hukumar Yi wa Malamai Rijista ta Ƙasa, TRCN, game wa’adin da TRCN ɗin ta sa cewa zuwa 2020 duk malamin da bai cancanta ba ko ba shi da rijista ba zai yi aikin koyarwa ba.

Sakataren Watsa Labarai na NUT, Emmanuel Hwande, ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ranar Laraba a Abuja cewa saka wa’adin ya zama wajibi don tabbatar da cewa malaman da suka cancancta ne kawai ke koyarwa a makarantu.

A ranar 7 ga watan Yuni, 2019 ne Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ta aika da takarda zuwa makarantu mallakin gwamnati dake cewa zuwa 31 ga watan Disamba, 2020, duk malaman da ba su cancancta ba za su bar koyarwa.

Maƙasudin shi ne a cire waɗanda ba su da ƙwarewa daga sana’ar koyarwa, da tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne kaɗai za su ba yaran ƙasar nan ilimi.

Mista Hwande ya ce NUT ta gamsu da yadda TRCN ke ƙoƙarin ganin an bi wannan umarni “saboda dole kowane malami ya zama ya cancancta kafin ya shiga aji ya koyar”.

A ta bakinsa, Najeriya na buƙatar malamai masu inganci ba “masu cutarwa” ba don bada ilimi mai inganci.

“An kafa TRCN ne don mayar da koyarwa wata sana’a da ba wanda zai iya yin ta sai wanda yake da cancancta.

“Idan kai ba ɗalibin da ya nazari Aikin Shari’a ba ne, kuma an kira ka zuwa Majalisar Lauyoyi, ba za ka iya shiga kotu ba; ya kamata a sa wannan a aikin koyarwa.

“TRCN ta ce ba gudu ba ja da baya game da manufar, Ƙungiyar Malaman kuma za ta ba Majalisar goyon baya ta kowace hanya da za ta yiwu don cimma muradinta saboda muna buƙatar malamai masu nagarta da za su bada ilimi mai nagarta”, in ji shi.

Mista Hwande ya ƙara da cewa yadda makarantun gwamnati ke bin wannan doka, ya fi yadda makarantu masu zaman kansu ke bi, waɗanda har yanzu ba su fara bi ba.

“Abinda ke hana makarantu masu zaman kansu guje wa dokar shi ne hukumomin gudanarwarsu, masu makarantun da tsoron kunyata ma’aikatansu.

“Wani lokaci a baya, NUT ta je don aiwatar da aikinta da doka ta ɗora mata a tsarin makaranta, amma an samu tirjiya sosai daga makarantu masu zaman kansu.

“Mun tattauna da gwamnati a ciki don gabatar da buƙatunmu, idan kuma gwamnati ta mayar da martani, ba za mu bar batutuwan ba ko wasu, wannan shi ne tsoron makarantu masu zaman kansu”, in ji Mista Hwande.

Mista Hwande ya ce lokaci da yawa NUT takan tura wa makarantu masu zaman kansu takardun neman bahasi bisa yadda suke ɗaukar malamai, saboda irin mutanen da suke ɗauka ba su da dabarun koyarwa.

“Idan suna ɗaukar masu Digiri na Biyu, ba za su iya biyan su ba. Abinda suke yi shi ne sai su ɗauki wanda ke da Takardar Kammala Sakandire ta WAEC da NECO.

“Koyarwa aiki ne na ƙwararru, ba za ka iya kai Takardar Shaidarka ta WAEC ko NECO zuwa asibiti ba a matsayin likita ko malamin jiyya ba, ba wanda zai ƙyale ka.

“Dole a cire marasa ƙwarewa daga cikin aikin koyarwa don cimma muradin TRCN na bayyana su wane ne malamai ta fuskar cancanta da rijista da Hukumar”, in ji shi.

Mai magana da yawun Ƙungiyar ya bayyana cewa idan wa’adin ya ƙare, jami’an Ƙungiyar da TRCN za su je makarantun gwamnati da masu zaman kansu don tilasta aiki da dokar.

Ya roƙi malaman da abinda ya shafa da su yi amfani da damar gwaji da za a yi su yi abinda ya dace kafin cikar wa’adin “saboda da zarar an kama ka a matsayin malamin da bai cancanta ba, hukumomi za su ɗauki hukunci.

Game da umarnin Sashin Hada-hadar Kuɗi na Nigeria Financial Intelligence Unit, NFIU cewa dole dukkan kuɗaɗen ƙananan hukumomi su shiga asusunsu na banki kai-tsaye, Mista Hwande ya ce wannan umarni zai dawo da ilimin firamare shekarun da suke kafin 1994.

A ta bakinsa, wannan shi ne lokacin da ake amfani da kuɗin albashin malamai ga wasu buƙatun.

“Wannan ya riƙa sa malamai su riƙa bin bashin albashi na watanni 10 zuwa 12 a wasu jihohi.

“Matsayar NUT game da wannan shi ne duk wani abu da gwamnati za ta aiwatar kada ya shafi biyan albashin malmai.

“Jiha ita ce take da haƙƙi game da kula da ilimin firamare, abinda ƙaramar hukuma ke yi shi ne ta haɗa kai da jiha don hana ilimin firamare durƙushewa a ƙarƙashin majalisun ƙananan hukumomi.

“Matsayinmu ne cewa dole a yi shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da sakin albashin malamai kafin a raba wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan