Home / Addini / NAHCON ta bayyana adadin alhazan Najeriya da suka samu kulawa daga likitoci

NAHCON ta bayyana adadin alhazan Najeriya da suka samu kulawa daga likitoci

Tawagar Likitocin Hukumar Aikin Haji ta Najeriya, NAHCON sun kula da alhazai 4,456 a kwanaki 14 bayan kafa ƙananan asibitocin kula da alhaza a Makka da Madina.

Shugaban Tawagar Likitocin ta NAHCON, Dokta Ibrahim Khana ya bayyana haka ga Masu Ɗaukar Rahoton Aikin Haji ranar Laraba.

A cewarsa, kawo yanzu an kafa ƙananan aisbitoci 10, 6 a Makka, 4 a Madina.

Kawo yanzu, alhazai 35 suna kwance a asibiti, yayinda aka mayar da 58 ga Asibitocin Saudiyya don ci gaba da ba su magani.

Haka kuma, Mista Khana ya ce Sashin Fasahar Sadarwa na NAHCON, wato ICT Unit ya samar da Na’urorin GPS don taimaka wa alhazai gane Cibiyoyin Kula da Lafiya na Najeriya dake Makka.

A cewar NAHCON, kawo yanzu an kai alhazai sama da 20,469 zuwa Saudiyya don sauke farali.

About Hassan Hamza

Check Also

Za A Cika Azumi 30 A Saudiyya

Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a dukkan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *