Gwamnan Bauchi ya angwance da ‘yar Lebanon

135

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya auri wata budurwa da aka yi imani cewa ‘yar ƙasar Lebanon ce mai zama a Najeriya.

Da yake bayyana haka a shafinsa na Facebook, Ladan Salihu, wanda shi ne mai magana da yawun Gwamnan, ya ce an ɗaura auren ne a Syrian Mosque dake kan Titin Ribadu a Jihar Legas.

Mista Salihu ya haɗa hotunan ɗaurin auren, dake nuna Gwamnan, Mista Ladan ɗin da kansa, mahaifi da wakilan amaryar da sauran abokan Mista Mohammed.

Amaryar za ta zama matar Gwamnan ta biyu.

A yanzu, Mista Mohammed shi ne gwamna na biyu da ya yi aure jim kaɗan bayan shiga ofis.

Ya bi sawun Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe wanda shi ma ya yi aure jim kaɗan bayan ya zama gwamna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan